Buhari ya nuna alhininsa game da mutuwar Pele

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya nuna alhininsa dangane da mutuwar gwarzon ɗan wasan ƙallon ƙafar nan na ƙasar Brazil, Edson Arantes do Nascimento, wanda aka fi sani da Pele.

Pele ya rasu ne a ranar Alhamis bayan fama da cutar kansa.

Cikin saƙon ta’aziyyar da ya aika a madadin ‘yan Nijeriya, Buhari ya yi fatan mutuwa ta zama hutu ga marigayin.

Ya kuma bayyana shi a matsayin wanda ya ba da gudunmawa mara misaltuwa a duniyar ƙwallon ƙafa da ma fannin wasannin motsa jiki baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa, marigayin ya taka rawa wajen samar da maslaha a ƙasashe da dama.

“Pele dai ya tafi amma duniya ba za ta mance da shi ba,” in ji Buhari.

A halin rayuwarsa, sau uku Pele na lashe Kofin Duniya.

Sannan ya zira ƙwallo sama da 1,281 a raga a tsakanin wasannin da buga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *