Gwamnati na aiki tuƙuru kan karɓo sauran ‘yan matan Chibok – Minista Sadiya

Daga AISHA ASAS

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta na ci gaba da aiki ba tare da gajiyawa ba domin ta ceto sauran ‘yan matan Chibok waɗanda aka sace shekaru bakwai da su ka gabata.

Ministar ta yi wannan maganar ne a ranar Laraba lokacin da ta ke jimamin abin baƙin cikin nan da ya faru na satar ɗaruruwan ‘yan matan daga makarantar su ta kwana da ke garin Chibok a Jihar Borno.

Mayaƙan Boko Haram ne su ka sace ‘yan matan.

Sadiya Farouq ta ce ta na matuƙar alhinin abin da ya faru kuma ta yi addu’ar Allah ya sada sauran ‘yan matan da aka sace da iyalan su nan ba da daɗewa ba.

Ta ce, “A matsayi na na Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, ina jin zafin a ce an cika shekaru bakwai tun da aka sace ‘yan matan Chibok. 

“Gwamnatin mu ta samu mulki ne bisa hurumin jama’a na kawo ƙarshen ta’addanci a yankin Arewa-maso-gabas wanda shi ne ya janyo sace ‘yan matan na Chibok kuma ta yaƙi cin hancin da ya hana a yi aikin ceto su.

“Mun samu nasara sosai, to amma har yanzu akwai sauran aiki ga dukkan matakan gwamnati. An ceto rabin yawan ‘yan matan an sada su da iyalan su kuma sun ci gaba da makaranta. Za mu ci gaba da aiki domin mu dawo da sauran waɗanda su ka rage.”

Ministar ta yi la’akari da cewa gwamnatoci a matakan ƙaramar hukuma, jiha da kuma tarayya sun inganta abin da su ke yi idan an kai hare-hare a makarantu kuma su na aiki bakin ƙarfin su don hana kai hare-haren.

“Ba zan iya bayyana irin dabarun tsaro da matakan da ake ɗauka a fili ba, amma ina tabbatar maku da cewa gwamnati ta ɗauki tsaron lafiyar jama’ar ta a matsayin muhimmin aiki. Mu na yaƙar ambaliyar ayyukan laifi ne da zazzafan tsattsauran ra’ayi a yankin tare da haɗin gwiwar wasu.  

“Bari in kwantar wa da iyayen yarinyar Chibok ɗin nan, Leah Sharibu, da na sauran waɗanda aka kama cewar wannan gwamnatin ba ta manta da ku ba. Mun ji buƙatun ku, kuma ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa za su yi wani abu a madadin gwamnati.

“Dukkan ‘ya’yan mu sun cancanci a ba su ilimi. Ƙasar mu na buƙatar a ilimantar da su don ci-gaban mu. Babu wanda za a ce ya zaɓi ko dai makaranta ko zaman lafiya.

“Za mu yi dukkan abin da ya kamata don mu ba kowane yaro ɗan Nijeriya damar ficewa daga ƙangin fatara kuma ya cimma burin rayuwar sa.”

A ranar 14 ga Afrilu, 2014 ne dai ‘yan ta’adda su ka kama ‘yan mata 276 a cikin dare a Makarantar Sakandare ta Chibok, su ka gudu da su.