Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bukaci kafafen yaɗa labarai da su riƙa yin magana kan asalin cigaban da ake samu wajen yaƙi da matsalar tsaro, ya ce, domin kuwa ana samun muhimman nasarori a yaƙin.
A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, a ranar Litinin, Buhari ya ce, ya kamata a maye gurbin kalmar ‘matsalar tsaro’ da ‘gaskiyar raguwar rashin tsaro.’
Takardar mai taken, ‘Shugaba Buhari ya taya Musulmai murna a ranar Mauludi, ya tabbatar da cewa ana samun muhimman nasarori a yaƙi da rashin tsaro.’
A wani ɓangare kuma an karanta cewa, “Shugaban ya buƙaci Musulmai da su yi ƙoƙarin neman gafara da kusanci da kyakkyawar rayuwa da koyarwar Manzon Allah (SAW) wanda ake murnar ranar haihuwarsa a wannan rana mai albarka. A kan wannan lokaci mai albarka, ina yi muku fatan albarkar yau.
“Shugaban yana amfani da wannan damar don bayyana irin ayyukan da Sojoji, ‘yan Sanda, da hukumomin leƙen asiri suka fara don shawo kan ƙalubalen tsaro a cikin ƙasar.
Ya ce gwamnati na da niyyar ci gaba da wannan aikin, kuma tana kira ga kafofin watsa labarai don magance matsalolin,” inji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Shugaban ya ƙara da cewa ƙarin haɗin kai da haɗin gwiwa daga ‘yan ƙasa, haɗe da ƙarfafa gwiwa, ƙwazo, da ƙarfafa gwiwar ‘yan sanda, tsaro da jagorancin sojoji na taimakawa gwamnatin samun nasarori da yawa kan ta’addanci, aikata laifuka, da lalata tattalin arziki.
Haƙiƙanin raguwar rashin tsaro ya kamata ya maye gurbin labarin da ba daidai ba game da hauhawar rashin tsaro a ƙasar.
Shehu ya nakalto Buhari yana cewa, “duk da yake akwai aikin yi, maza da mata sanye da kakin soji da ke taimakawa al’umma, don cimma wannan burin, suna son jin daɗin mu tare da ƙarfafa gwiwa don yin hakan.”
Shugaban ya ƙarƙare saqon nasa inda ya yi kira ga masu amfani da hanya da su yi tuƙi cikin kulawa tare da kaucewa haɗurra marasa amfani.