Dokar kiwo a Kudu: Makiyaya sun fara hijira zuwa Arewa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Sakamakon sanarwar da mafi yawan gwamnonin kudancin Nijeriya suka bayar na hana Fulani makiyaya gudanar da kiwo a jihohinsu ta sa dubban Fulani yin hijirar dole zuwa Arewa, musamman daga jihohin Oyo, Osun, Ogun, Ondo, Lagos da Ekiti.

Wakilin Manhaja a Jihar Jigawa ya gane wa idonsu yadda makiyayan suke tururuwa shiga jihar Jigawa daga jihohin Yarabawa da Igbo bayan da suka yi kiran da su fice su bar mu su yankunansu.

Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah, reshen Jihar Jigawa, Alhaji Adamu Idris Babura, ya ce, shi da kansa ya gane wa idonsa ‘yan uwansa makiyayan suna ta komo wa gida daga yankunan Yarabawa da Igbo.

Ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi tanadin sama wa Fulani ruwan kiwo a dazukan kiwonsu na jihar tare da samar da ciyayin kiwo, domin amfanin dabbobinsu.

Ya ƙara da cewar, duk Fulani suna ta dawowa kuma an yi tanadin amsar su babu wata matsala.

Don haka ya hori Fulanin da su zauna da ‘yn uwansu manoma lafiya kuma su guji yi wa manoma ta’adin ganganci, saboda a samu ɗorewar zaman lafiya mai ma’ana.

Alh. Adamu Idris Babura

Ya ci gabada cewa, su na nan su na shirin kafa wani kwamiti da zai haɗa da dillalan shanu da manyan ‘yan kasuwa da masu faɗa-a-ji da za su ɗauki matakin ramuwa akan matakin da gwamnonin Yarabawa da suka kori makiyaya daga jihohinsu.

Ya tabbatar da cewar za su ɗauki matakin da za a daina kai naman shanu kudancin Nijeriya a wani mataki na yin ramuwar gayya akansu.

Ya ci gaba da cewa, uwar ƙungiyarsu tana nan tana bin matakai daki-daki da za ta fito da jadawalin shirye-shirye akan irin matakan da za su ɗauka.