Daga BABANGIDA S. GORA a Kano
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Abubakar Lawal ya fara gudanar da ziyara domin karɓar ƙorafe-ƙorafen da jama’ar yankunan suke da shi akan harkar tsaro tare da karɓar koken nasu don magance shi cikin gaggawa.
Daura wanda ya fara da shiyyar Area Command ta Metro ta hannun shugabancin kwamitin aikin tsaro da al’umma (PCRC) yayin da su ka bayar da wata mota domin tallafawa jami’an ‘yan sandan wajen gudanar da ayyukan su tare da da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Shi ma a nasa jawabin shugaban kwamitin aikin tsaro da al’umma Alhaji Ahmad Sufi ya bayyana cewa “Jihahar Kano duk wanda ya duba sai ya tabbatar da cewa akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali sakamakon irin ƙoƙarin gwamnati Jihar Kano da jami’an tsaro.
Sufi, ya yi kuma matuƙar godiya ga al’umma da malamai bisa addu’o’in da suke yi a kodayaushe don samun zaman lafiya.
“Muna kira ga al’umma da su ƙara tallafa wa jami’an tsaro da abinda Allah ya hore ma su don cigaba da wanzar da zaman lafiya.”
CP Abubakar Lawan ya ce wannan mota da ƙungiyar PCRC ta bayar ya tabbatar da cewa suna taimaka wa harkar tsaro domin ya gani a ƙasa.
Kwamishinan ya kuma yaba wa jami’an ‘yan sanda bisa yadda suke aikin tsaro da al’umma har ma ya ja kunnen su ,duk lokacin da wakilan al’ummar suka zo wajensu su saurare su don ɗaukar mataki a kan matsalar da suke da ita .
“Daman Jihar Kano waje ne na kasuwanci, domin idan babu tsaro harkar kasuwanci ba zai yiwu ba, don haka dole muka ra ƙaimi wajen samar da tsaro.”