Me ya sa aka dakatar da koyar da ilimin jima’i a makarantu?

Manhaja logo

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ba da jimawa ba ne ofishin Ministan Ma’aikatar Ilimi Malam Adamu Adamu ya fitar da wata sanarwa game umarnin dakatar da cigaba da koyar da ilimin jima’i a ƙananan makarantu da sanarwar fara amfani da harshen uwa na gado wajen koyar da yaran makarantun firamare, a tsarin koyarwa na makarantun ƙasar nan. Batutuwan da yanzu haka ke cigaba da ɗaukar hankalin masana ilimi da sauran jama’ar ƙasa.

A wannan mako nima ina son yin tsokaci ne game da batun dakatar da koyar da ilimin jima’i a makarantu, kamar yadda taken rubutun ya nuna, domin qara fayyace yadda lamarin yake da tasirin wannan mataki kan harkokin koyarwa da inganta tarbiyyar yaran mu manyan gobe.

Ministan kamar yadda ya faɗa a Babban Taron Majalisar Kula da Harkokin Ilimi ta Ƙasa karo na 66 a Babban Birnin Tarayya Abuja, wasu daga cikin abubuwan da ake koyarwa a makarantu game da ilimin jima’i sun sava da koyarwar addini da al’adun al’ummar ƙasar nan, kuma cigaba da koyar da irin waɗannan abubuwa cigaba ne da gurvata tarbiyyar yara masu tasowa da matasan ƙasar nan.

Ya ce, “A lokacin da na raka Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zuwa Birnin New York a ƙasar Amurka, wani babban jami’in gwamnati ya ja hankalina kan wasu abubuwa da ke ƙunshe cikin tsarin koyar da ilimin jima’i da ake karantarwa a makarantun Nijeriya, gaskiya ganin waɗannan abubuwa na girgiza sosai, kuma hankalina ya tashi sosai. Ko da yake ba wai ina ƙyamar koyar da ilimin jima’i a makarantun mu ba ne, sai dai ina ganin akwai wasu hanyoyi da dabarun da suka fi dacewa a ilimantar da yara abubuwan da suka shafi lafiyarsu da rayuwarsu. Sannan abin da ya shafi jima’i da makamancin haka zai fi dacewa idan manya ake koyawa ba ƙananan yara ba.

Malam Adamu Adamu ya ƙara da cewa, mutanen mu na Afirka na ganin kamar duk wani abu da ya samo asali daga turawa to, shi ne cigaba da kuma wayewa. Alhalin mu a wannan yanki muna da wasu abubuwa da suke inganta rayuwar mu da tarbiyyarmu, su ne kuwa addini da al’adu, waɗanda idan muka yi riƙo da su, za mu samu tsaftace rayuwarmu, kuma tarbiyyar mu ta inganta.

Yanzu dai ta tabbata, ma’aikatar ilimi ta ƙasa ta bai wa hukumar kula da shirya jadawalin koyarwa a makarantu ta NERDC ta cire duk wani abu da ya shafi vangaren koyar da ilimin jima’i a makarantun ƙasar nan. Matakin da ƙungiyoyin sa kai na al’umma su 54 suka haɗu wajen ƙalubalantar wannan mataki na Gwamnatin Tarayya, bisa hujjar cewa hakan zai iya dawo da hannun agogo baya, a yaƙin da ake yi da yaɗuwar cutar HIV mai karya garkuwar jiki.

Masu goyon bayan wannan tsarin na ganin koyar da yara sanin ilimin jima’i zai taimaka musu wajen sanin mai ya kamata su yi a lokacin da wani babba ya afka musu da nufin fyaɗe ko masu lalata da ƙananan yara, daga cikin abokan karatu, gurɓatattun da wasu makusanta na gida ko na anguwa, musamman yadda cutar HIV mai karya garkuwar jiki take yaɗuwa, da sauran cututtuka da ake samu daga jima’i marar tsafta.

Har wa yau kuma, ana danganta matsalolin da yara mata da ke shekarun fara al’ada suke fuskanta, samun shigar cikin da ba a shirya shigarsa ba, ta dalilin fyaɗe ko yaudarar wasu maza, da kuma damuwoyin da ake samu yayin zubar da ciki ko amfani da magungunan hana ɗaukar ciki, kan rashin samun ilimin jima’i da wuri, da ba su shawarwarin da ya dace a kan lokaci.

Tun farkon shigo da wannan tsari kimanin shekaru 20 da suka gabata a makarantun Nijeriya, ya sha suka sosai a wajen malaman addini, masana tarbiyya da iyaye, waɗanda ke ganin illar yin hakan ga gyaruwar tarbiyyar ƙananan yara da ke tasowa da tunanin gwada duk wani abu da suke ji ko gani, domin tabbatar da yadda yake, ba tare da sun san illoli ko rashin dacewar hakan ba.

Ko da yake, sanin kowa ne wannan batu ne mai matuqar ɗaure kai ba ga malamai kaɗai ba har ma da iyaye waɗanda suka fi kusa da waɗannan yara, domin kuwa da zarar sun dawo gida daga makaranta, iyayen su ne suke fara tunkara da tambayoyi don fayyace musu abubuwan da malamansu suka gaya musu a makaranta. Kamar dai batun bambancin halittar mace da namiji da alamomin balaga a jikin mace ko namiji, misalin yadda yarona Aliyu ya dawo gida yana tambayata in gaya masa wuraren da gashi ke fitowa a jikin namiji ko mace in sun balaga! Ba duk uba ko uwa ne za su iya sakewa su yi wa ɗan su ko ’yarsu mai ƙananan shekaru irin waxannan bayanan ba, ballantana a je ga batun yaya ake ɗaukar ciki.

Lallai dole malamai da masu nazari kan harkokin ilimi su koka ga irin wannan tsari na koyarwa da bai dace da ƙananan yara da ba su balaga ba, ko kuma suke da ƙananan shekaru, domin tasirin da hakan ke da shi ga tarbiyyarsu da tunanin su. Wannan tattaunawa ba kasafai iyaye ke zama su yi shi da yara ba, saboda kunya da al’ada. Kamar yadda mahaifiyar Zainul Abideen ta kasa natsuwa ta saurari tambayoyin da ɗanta yake yi wa babansa ba. Fahimtarta tayi daidai da tawa, inda muke ganin wannan koyarwa ba ta dace da ƙananan yara irin sa ba.

Ko da yake mun taso a al’adance a nan ƙasar Hausa sai yaro ya girma har ya kusa balaga ne sannan yake fara sanin wasu abubuwan, kafin wani wansa ko malaminsa na Islamiyya ya fara koya masa abubuwan da, suka wajaba a kansa na game da ayyukan ibada da zaman aure. Haka ita ma mace daga lokacin da ta fara jinin al’ada, a lokacin ne mahaifiyarta ko ƙanwar mahaifiyar ta ke sanar da ita wasu abubuwa da ya kamata ta kula da su, da kuma a makaranta wajen karatun ilimin addini, inda malaman fiƙhu suka yi bayani dalla dalla, game da hukuncin addinin Musulunci a game da waɗannan muhimman batutuwa da suka shafi al’ada, balaga, jima’i da zamantakewar aure.

Yadda rayuwa ta canza a halin da ake ciki, abubuwa na ilimomi na nan birjik a kafafen sadarwa na zamani, wanda ba ka buƙatar zaunar da yaro ka koya masa wani abu, sai dai ƙoƙarinsa masa ido da tarbiyyar da shi a kan tsarin addini da halayen ƙwarai, don kada ya yi amfani da ilimin da yake gani a yanar gizo ta inda bai dace ba.

Allah ya tsare zuciyoyin mu da rayuwarmu da ta iyalin mu, daga sharrin zamani da gurvacewar rayuwa. Amin.