Makamashi: Da sake amba mai kaza kai

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Tsarin mulkin ƙasar nan ya tanadi tsare-tsare masu tarin yawa domin ya daga ƙasar da al’umarta a idan duniya, amma abin takaici abin bah aka yake ba. Babban abin takaici, shugbannin ƙasar tun daga kansila har zuwa shugaban ƙasa babu ruwansu da waɗanda suke shugabanta.

Tasarrafi da dukiyar ƙasa, wato bitalmali ya zama abin watanda da ga shugabanni saboda haka kowa sai wasa wuƙaƙensu da gatarai a dandalin siyasa domin kawai su sami dama su gididdibi tasu karfatar yaran su suna biye dasu domin fince. ‘Yan ƙasa sun zama ‘yan kallo. Wannan tasa muke cewa “Da sake amba mai kaza ki”.

Saboda wannan taɓargaza da wadaƙa dukiya daga hanya daya tilo, makamashin man fetur da gas da Nijeriya take fitarwa da sama da ganga miliyan guda a kullum zuwa kasuwar duniya, banda ma’adanai da kuma amfanin gona na biliyoyin nairori, wannan tasa Bankin Duniya da Hakumar nan mai bayar da lamuni ga ƙasashe suka yi kididdiga cewa da shugabannin Nijeriya masu adalci ne a mulkin su kowanne ɗan Nijeriya zai sami Dalar Amurka sama da Dala Dari (100) a kullum.

Dala ɗari a yanzu, ta kai sama da Naira dubu ɗari da talatin (₦130,000) dan Nijeriya zai riƙa samu a kullum, amma abin bakin ciki yau ɗin nan ‘yan Nijeriya sama da kashi (80%) cikin dari (100%) bas a samun Dala Ɗaya wato dubu daya da ɗari uku (₦1,300) a kullum. Wannnan ake cewa “mai doki ya koma kutiri” wannan take tabbatar da cewa dole da sake amba mai kaza kai. Idan baso ake bijirewa ta mbiya ta biyo bay aba, kamar yadda tarihi yake nunawa yana faruwa ga shugabanni azzalumai.

Babu abinda talauci yake haifarwa, illah yunwa ita kuma yunwa dandali ne na fituntunu cin hanci, rashawa, sace-sace, fashi da makami, kasha-kashe babu gaira babu dalili, yaƙi a cikin gida, yankewar zumunci a tsakanin al’umma ko tsakanin ƙasa da ƙasa. Talauci shi yake haifar da da marar ido, saboda haka si rashin da’a ya sami ginding zama, wannan lokaci ne rayayye yake sha’awar na kabari.

Da sake a Nijeriya, muna da makamashi na man fetur da gas da zai shayar da dukkan nahiyar Afirka ko da kuwa babu wata ƙasa da take da digo daya na wannan makamashi. Baya ga haka, “uranium deposit” da ba fara tonarsa ba a Nijeriya zai sha kan wanda ake tona yanzu a jamhuniyyar Nijar da Namibiya da Africa ta kudu. Da shugabannin Nijeriya zasu yi wa kansu adalci da Nijeriya ta zama ljannar duniya dga wannan ma’adanai ko makamashi.

Da adalci na shugabanni da yanzu Nijeriya na kan gaba a fannin ma’adanai (minerals), babu wata ƙasa a Afrika da zata yi takara da mu. Wannan hali na rashin hangen nesa muke cikin wannan tsanani na talauci da yunwa da kuma cututtuka. Kuma yanzu an shigo da wata annobar mai wuyar magani, wato hahhawar farashi a kasuwanni, kullum si farashi ya tashi daga yadda ka san shi a jiya da shekaranjiya da suka fuce, kuma ba zaka san nawa farashi zai kasance ba gobe ko jibi ba.

Wannan annoba wutar daji ce, dai dai suke da yunwa fyade yaro fyaɗe babba, ita masu hikima a rayuwa suke yi mata da kirari da “bata jin lahaula” sai dai a bata dimamai ko kuwa loma guda ne. rashina da’ami ga ‘yan ƙasa babu abin da yake haifarwa sai bore da tarzoma daga nan sai wawaso na dukiya sai kuma koma baya ta afku na tsahon shekaru 30 zuwa 90 kafin a shawo kan wannan asara.

Nijeriya na buƙatar shugabanni Jajirtu masu hangen nesa kuma masu sadaukar da kawunan su ko da kuwa za su yi asarar rayukan su ne da kuma dukiyar su suka san ce, basu da wata alƙibla sai kawai Nijeriya da ɗan Nijeriya ko da kuwa za su ƙara wani abu sai wannan nahiyar tamu ta Afirka. Su kuma mabiya ‘yan ƙasa dole su zama masu biyayya ga umarnin shugabbani, ma’ana idan suka yi doka suka ce ayi kaza wajibi ne ga ‘yan ƙasa su yi wannan abu.

Idan kuwa suka yi hani, shima ya zama wajibi ga duk ɗan ƙasa na gari ya yi biyayya ya guji wannan abu. Idan kuma yayi biris da wannan hai sai a hakunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Babban misali cin hanci ko rashawa ko babakere da dukiyar ƙasa ko kuma ribda ciki ko kuma wasarere da wannan dukiya sai a hukunta shi ko a hakunta su. Hakuncin nan kuwa ko asarar rayukan su za su yi kamar yadda su shugabanni suka ba da rayukansu saboda kasa.

Kamar yadda muke fada a kullum a wannan fili dukiyr kasa makamashi da Allah ya horewa wannan kasa musamman ma man fetur da gas da sauna dangoginsa wanda ‘yan Nijeriya za su dogara dashi dari bisa dari sun yi sallama ta ban kwana da talauci da yunwa da jahilci da cututtuka, amma wasu ‘yan kalilan su wawashe babu ta ido kuma babu tsoran Allah, wannna babban kuskure ne.

Wajibi ne mu farka, farkawa ta ba mu yarda ba, wato da sake kamar yadda muka ce tun farko wannan batu “da sake amba mai kaza kai” a Nijeriya ko kan ba’a bashi yana kallo ana wadaƙa da haƙƙin sa. Wannan batu na bamu yarda ba, ba batu bane na mayaudara waisu “whistle blowers” masu ci da gumin wasu da suna ye daban daban. Saboda haka wannan farkawa tafi ƙarfin masu rajin wata aƙida ko daga ina ta fito.

Talakan ƙasa shi zai sauya taku tun da kiɗa ya sauya sai takun rawa ya sauya, tunda shugabanni san zama barayin zaune masu ci da biro, wato alƙalama. Mutane su sanya alƙalama su kwashi dukiyar kasa sub a su ci ba kuma ba su bawa na kusa dasu ba, amma sun kaiwa wasu ‘yan tasha a ingila ko faransa ko kuma uwar gijiyar su amurka, ko kuma wasu sabbin ɓarayi daga china, wato ƙasar sin ko rasha tsohuwar Tarayyar Soviet.

Amurka da duk wata ƙasa ta yammacin turai da kuma ƙasashe masu da’awar aƙidar gurguzu ko kuma ita akidar domakaraɗiyya sammakal bakin su ɗaya a ɓoye dababrune na jida da kwarkwasar dukiyar marar wayo. Saboda haka wajibi ne mu yi koyi da faɗakarwar NEPU da PRP da yake cewa “wayo shima ya san naki” don haka a sanar da Amurka da ‘yan kanzaginta cewa daga yanzu “munki da duk wani tsari da ya zo daga gurinsu”.

Lokaci ya yi da talakan Nijeriya zai koyi aƙidar na ƙi, banyarda a ci gaba da yaudarar ‘yan kasa da sunanan yajin aiki daga wata ƙungiya ba, wala wannnan kungiyar ta ƙodago ce ko kuma ta rajin damokaraɗiyya ko kuma rajin wani tsari a bayyane (bude) duka yaudara ce, muce munki. Sannu a hankali zaka tarar an kawo sauyi cikin sauƙi ba tare da rudani ba.

Farkon fari shine mun daina ciniki da kowacce ƙasa da Dalar Amurka, zamuyi ciniki ne da ɗai-ɗaikun jama’a da hakumomi a ƙasa da kuɗin ƙasa kasashe su kuma za mu yi ciniki a tsakanin mu bisa tsarin wadannan ƙasashe kamar yaddda ake yi ada na cinikin bani gishiri na baka manda. Wato na ba ka man fetur ka bani takin zamani ko dabbobi ko alƙalma da ni kuma zan yi fulawa saboda masu sana’ar cimaka.