Mamu ya nemi gwamnati ta janye ayyana shi da aka yi a matsayin mai taimaka wa ‘yan ta’adda

Daga BASHIR ISAH

Mawallafin Jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, ya buƙaci gwamnati ta janye ayyana shi da ta yi a cikin jerin masu taimaka wa ‘yan ta’adda a ƙasar nan.

Mamu ya buƙaci hakan ne a cikin wasiƙar da ya aike wa Babban Lauyan Nijeriya mai ɗauke da kwanan wata 25 ga Maris, 2024.

Lauyansa, J.J. Usman (SAN), shi ne ya rubuta wasiƙar a madadinsa, wanda a ranar Talata Jaridar News Point Nigeria ta samu ganin shaidar karɓar kwafin wasiƙar da aka aike wa AGF a Kaduna.

Kwanan nan ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana sunayen wasu mutum 15 ciki har da kamfanonin da take zargi suna da hannu wajen taimaka wa ‘yan ta’adda wajen gudanar da harkokinsu.

Sai dai kuma, lauyan Mamu ya ce, “Kwamitin Kafa Takunkumi na Nijeriya ba shi da hurumin ayyana Tukur Muhammad Mamu a matsayin mai taimaka wa ‘yan ta’adda.”

Bugu da ƙari, wasiƙar ta nuna wa’adin kwana bakwai kacal aka bayar kan a janye ayyana Mamu da aka yi a matsayin mai taimaka wa ‘yan ta’adda.

Lauyan ya ƙara da cewa, a halin da ake ciki, AGF na shari’a da wanda yake karewa bisa zargin taimaka wa ‘yan ta’adda.