Sabuwar barazanar Boko Haram: Nijeriya na buƙatar tsauraran matakai don tabbatar da cikakken zaman lafiya

Spread the love

Sabuwar barazanar da wasu ‘yan ta’adda suka yi na kai hari ko tayar da bom a Majalisar Dokokin ƙasa ta sake tayar da hankalin jama’a. Wannan barazana ba ta fito daga iska ba — alama ce ta cewa har yanzu akwai ƙananan ƙungiyoyin da ke ƙoƙarin sake farfaɗowa bayan an raunana su ta hannun dakarun gwamnati. Amma wannan lokaci daban ne, saboda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta nuna cewa ba za ta lamunci kowace irin barazana ga tsaron ƙasa ba.

A matsayinta na cibiyar dokoki da ginshiƙin dimokuraɗiyya, Majalisar Dokoki ba kawai wurin tattauna dokoki ba ce; ita ce zuciyar tsarin mulkin ƙasar. Don haka, duk wata barazana da za ta shafi amincinta ko tsaronta, ta shafi kowa kai tsaye — daga talaka har zuwa shugaban ƙasa. Wannan dalili ne ya sa dole a ɗauki wannan barazanar da matuƙar muhimmanci, ba tare da wasa ba.

Tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa manufar gwamnatinsa ita ce samar da ƙasar da ke da cikakken tsaro, wacce ‘yan ƙasa za su iya bacci cikin natsuwa. A ƙarƙashinsa, an sake tsari da dama a sashen tsaro, an yi sauye-sauye a manyan muƙaman soja, sannan aka kafa tsarin haɗin gwiwar bayanan leƙen asiri tsakanin rundunoni.

A yau, dakarun soji da ‘yan sanda sun fi samun kayan aiki fiye da yadda aka saba a baya. Ana amfani da jiragen leƙen asiri, sabbin na’urorin gano bama-bamai, da kuma ingantattun hanyoyin sadarwa. Shugaba Tinubu ya kuma ƙƙddamar da tsarin National Counter-Terrorism Centre (NCTC) da ke ƙarƙashin Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaro, wanda ke haɗa bayanan leƙen asiri daga sassa daban-daban domin mayar da martani cikin sauri.

Wannan ci gaba ya nuna jajircewar gwamnatin Tinubu wajen tabbatar da cewa Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci ba za su sake samun ƙarfi ba. A wasu yankuna na Arewa maso Gabas, musamman Borno da Yobe, jama’a sun fara komawa gidajensu bayan shekaru na hijira — alamar cewa ci gaba yana faruwa.

Sai dai sabuwar barazanar da Majalisar Dokoki ta bayyana ta nuna cewa har yanzu akwai ‘yan ta’adda da ke neman hanyoyin tada hankali. Ko da yake ana ganin Boko Haram ta raunana, ƙungiyar ta sake rarrabuwa zuwa ƙananan sassa da ke aiki ɓoye. Wasu daga cikin waɗannan ƙungiyoyi na iya samun kuɗi daga ta’ammali da makamai, haƙar ma’adanai da satar mutane.

Wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnati ba ta isa ta rage sa ido ba. A irin wannan lokaci ne ake buƙatar ƙarin tsauraran matakai, musamman a wuraren gwamnati da cibiyoyin taro. Tsaro ba kawai na sojoji da ‘yan sanda ba ne; ya haɗa da masu leƙen asiri, jami’an tsaron majalisa, ma’aikata, da jama’ar gari.

Wani muhimmin darasi da ake koya daga yaƙi da ta’addanci shi ne cewa babu wata gwamnati da za ta iya cin nasara idan al’umma ba su shiga ba. Jama’a su ne idanu da kunnuwan gwamnati. Kowane ɗan ƙasa zai iya taka muhimmiyar rawa ta hanyar bayar da rahoto idan ya ga abin da yake da shakku, ko kuma taimakawa jami’an tsaro wajen tattara bayanai.

Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin shugabancin Tinubu, ta kuma fara wani muhimmin shiri na Community Policing da nufin haca jama’a kai tsaye cikin tsarin tsaro. Wannan tsarin, idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata, zai rage nauyi a kan sojoji, ya kuma ƙara sa jama’a su ji suna da alhakin kare ƙasarsu.

A yau, yaƙi da Boko Haram ya wuce batun bindiga da harsashi kawai. Ya zama batun fahimta da dabaru — daga yaƙi da ra’ayoyin ƙarya da ke jawo mutane zuwa ƙungiyoyin ta’addanci, zuwa gyaran tsarin zamantakewa da tattalin arziki.

Yawancin waɗanda suka shiga Boko Haram sun fito ne daga yankunan da aka daɗe ana fama da talauci, jahilci da rashin aikin yi. Don haka, gwamnati tana da rawar da za ta taka wajen tabbatar da cewa an samar da ayyukan yi, ilimi da walwala domin kau da mutane daga faɗawa cikin hanyoyin ta’addanci. Wannan shi ne ainihin manufar da Shugaba Tinubu ya bayyana a cikin Renewed Hope Agenda — manufar da ke haɗa tsaro da tattalin arziki da walwalar jama’a.

Sabuwar barazanar Boko Haram ta kuma nuna buƙatar ɗaukar tsauraran matakai na tsaro a dukkan matakan gwamnati. Wajibi ne Majalisar Dokoki, Fadar Shugaban ƙasa, da ma’aikatun gwamnati su ƙarfafa tsarin binciken masu shiga, saka kyamarori na zamani, da kuma saka tsauraran ƙa’idoji kan masu ziyara.

A lokaci guda, hukumomin tsaro su ƙara haɗin kai wajen raba bayanai, saboda rashin haɗin kai na iya barin giɓi da ‘yan ta’adda ke cin moriya. Kamar yadda Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya jaddada a wani jawabi kwanan nan, “tattaunawa da masu ɗauke da makami ba tare da tilasta su ajiye makaman ba tamkar miƙa wuya ce.” Wannan magana gaskiya ce — domin duk wata tattaunawa ba ta da ma’ana idan har masu laifi suna riƙe da makami.

A wannan lokaci, dole ne a yaba wa gwamnatin Tinubu kan yadda ta ke tafiyar da batun tsaro cikin nutsuwa da dabaru. Ta guji yin hayaniya amma tana aiki da sakamako. Sojoji sun ƙara samun ƙwarin gwiwa, ‘yan sanda sun fara sabbin shirye-shirye na tunkarar laifuka, sannan gwamnatin Tarayya na haɗin kai da ƙasashen waje wajen amfani da bayanan fasaha da leƙen asiri.

A ƙasashen duniya, irin waɗannan shirye-shirye ne suka taimaka wajen rage ayyukan ta’addanci — kamar yadda aka gani a Afghanistan, Pakistan da Sahel. Tinubu na tafiya a wannan hanya, kuma abin yabawa ne.

Yaƙi da Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda ba ya buƙatar gwamnati kaɗai, yana buƙatar haɗin kai da fahimtar juna tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa. Kada mu sake yin sakaci. Duk wata barazana da aka samu ya kamata a ɗauka da muhimmanci. Hakan zai nuna cewa ƙasa na da haɗin kai, kuma ta shirya kare kanta daga kowace irin barazana.

Sabuwar barazanar Boko Haram wani gargaɗi ne da ke nuna cewa, ko da an samu ci gaba, har yanzu akwai ƙalubale. Amma gwamnatin Tinubu ta nuna cewa tana da ƙarfin gwiwa da jajircewa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Yanzu lokaci ne da ya dace a ƙarfafa matakan tsaro, a ƙara haɗin kai, a kuma tabbatar da cewa Nijeriya ba ta sake zama filin wasa ga ‘yan ta’adda ba. Idan aka ci gaba da wannan tafiya, babu shakka za a iya cewa nan gaba kaɗan, labarin Boko Haram zai zama tarihi a wannan ƙasa.

By ukarofi