Samo ’yanci ga fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da aka sace

Barazanar baya-bayan nan da ’yan ta’adda ke yi na kashe fasinjojin jirgin ƙasa da aka sace idan gwamnati ta gaza biyan buƙatunsu cikin kwanaki bakwai, dole ne a mayar da hankali a cikin gaggawa. ’Yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjojin da suke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022, sun bai wa Gwamnatin Tarayya damar tattaunawa da su tare da neman ganin an sako waɗanda aka sace. Sun yi gargaɗin cewa rashin yin hakan zai sa a kashe Waɗanda aka sacen.

’Yan ta’addan Waɗanda suka gabatar da buƙatar ta hannun Malam Tukur Mamu, kakakin wani fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmed Mahmud Gumi, ya bayyana cewa, sun yi garkuwa da mutanen ne a matsayin ramuwar gayya ga kamawa da tsare ’ya’yansu da jami’an tsaro suka yi. Sun yi watsi da batun kuɗi a tattaunawar, sun kuma dage kan cewa kafin tattaunawa mai ma’ana kan sakin fasinjojin da kuma dawo da zirga-zirgar jiragen qasa daga Abuja zuwa Kaduna lafiya, dole ne a sako ’ya’yansu da ake zargin an tsare su a wani wurin da ake tsare da su a Yola ba tare da wani sharaɗi ba.

An ruwaito shugaban ƙungiyar ta’addancin, Abu Barra, ya sha alwashin cewa, “sai an yi hakan ne kawai za mu sako wasu daga cikin waɗanda muka sace, musamman mata, yayin da za a sako sauran fasinjojin a musayar fursunoni da wasu abokanmu da gwamnati ke tsare da su.”

Barazanar masu garkuwa da mutanen ta zo ne watanni biyu bayan harin da wasu ’yan bindiga suka kai kan jirgin ƙasa da ke kan hanyar Abuja/Kaduna, inda aka kashe wasu fasinjoji tare da yin awon gaba da wasu yayin da aka bayyana ɓacewar wasu. Daga cikin Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da shugaban matasa na jam’iyyar APC mai mulki, Amin Mahmoud, likitan haƙori, Dr. Chinelo Megafu, lauya mai tasowa kuma ɗan babban lauyan Nijeriya, Tibile Mosugu, da Musa Lawal-Ozigi, sakatare-Janar, Ƙungiyar Kasuwanci (TUC). Bayan kai harin, hukumar kula da layin dogo ta Nijeriya (NRC) ta dakatar da ayyukan hanyar.

Lamarin ya faru ne kwanaki biyu bayan da wasu ’yan bindiga suka kai farmaki a filin jirgin sama na Kaduna, inda aka kashe ma’aikatan hukumar kula da sararin samaniyar Nijeriya (NAMA) tare da yin garkuwa da wasu ma’aikata. A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne wasu ’yan bindiga da ke aiki a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja suka lalata wani ɓangare na titin jirgin da bama-bamai, lamarin da ya tilasta wa hukumar NRC dakatar da ayyukan hanyar a karon farko.

Barazanar da ’yan ta’addan ke yi, bai kamata gwamnati ta nuna halin ko in kula a hakan hakan ba, kuma ya kamaya ta ɗauki matakin da ya dace. Abin baƙin ciki ne cewa fiye da watanni biyu da ƙazamin harin da ‘yan bindigar suka kai, gwamnatin Nijeriya ba ta ɗauki wani kwakkwaran mataki na ceto waɗanda lamarin ya shafa ba.

Cigaba da zaman waɗanda abin ya shafa a ragon masu garkuwa da mutane wata alama ce ta gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasar. Halin da su ke cikin a hannun garkuwar kamar yadda aka nuna a faifan bidiyo na baya-bayan nan da waɗanda suka sace su suka fitar abu ne mai ban tausayi da ban tsoro. Kada wani ɗan Nijeriya ya mutu a hannun ’yan ta’adda. Muna kira ga gwamnati da ta yi duk abin da za ta iya don ganin an ’yantar da waxanda aka sace. Dole ne gwamnati ta tabbatar da cewa ’yan ta’adda ba su aiwatar da barazanarsu ba. Lokaci yana da muhimmanci a wannan fannin.

Tuni dai iyalai da ’yan uwan ​​waɗanda aka sace suka shiga cikin mawuyacin hali sakamakon sace su da kuma barazanar da ‘yan ta’addan ke yi na kashe su idan gwamnati ta kasa biya musu buqatunsu. Abin takaici ne yadda ’yan ta’adda da ’yan fashi ke ƙara ƙaimi da dabarun kai hare-hare a ƙasar. Yawan hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa kan muhimman ababen more rayuwa na sufuri da kuma tsere mutane da su ke yi, yana yin tasiri sosai ga tattalin arzikin ƙasar. Hare-haren na iya zama alamar al’ummar da ke cikin ƙunci ne kawai.

Barazanar za ta cigaba da wanzuwa idan gwamnati da hukumomin tsaro da abin ya shafa ba su daƙile wannan lamari ba. Ya kamata gwamnati ce kawai ta mallaki kayan makamai, musamman wajen tabbatar da doka da oda.

Ya kamata jami’an tsaro su tashi tsaye wajen ganin sun magance ’yan ta’addar da ke addabar mutane a hanyar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna, su tabbatar ba su da hanyar da za su bi. Bai kamata a bar wani gurbi ba wajen tabbatar da cewa an sako waɗanda aka yi garkuwa da su.

A kai yaƙin zuwa ƙofar masu garkuwa da mutane domin ya zama kange ga sauran masu laifi da ke tunanin irin wannan mugun aiki. Bai kamata gwamnati ta ba da kai bori ya hau ba, amma ta tabbatar da cewa an ceto waɗanda aka sace.