Shugaban Ƙungiyar Ohanaeze, George Obiozor ya kwanta da dama

Daga WAKILINMU

Shugaban ƙungiyar nan ta ƙabilar Ibo Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor ya rasu.

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma ne ya sanar da mutuwar cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba da daddare.

Ya ce, “A madadin gwamnati da al’umar Jihar Imo, ni, Sanata Hope Uzodimma, Gwamnan Jihar Imo na sanar da rasuwar Shugaban Ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor ga duniya.

“Farfesa George Obiozor , fitaccen masani, dattijo kuma uban ƙasa ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

“Rasuwar shahararren jagoran Igbon kuma tsohon jakadan Nijeriya a Amurka, babban rashi ne ga Jihar Imo, yankin Kudu maso Gabas da ma Nijeriya baki daya,” in ji shi.

A ƙarshe, Gwamnan ya ce za a sanar da lokacin da za a yi jana’izar marigayin nan ba da jimawa ba, tare da addu’ar mutuwa ta zama hutu a gare shi.

An zabi Obiozor a matsayin shugaban Ƙungiyar Ohanaeze ne a watan Janairun 2021, inda ya gaji John Nnia Nwodo.