Siyasar talaka

Tabbas talakawa ne a gidan gaba wajen yin sanadin samun nasara ga duk wani wanda ya fito takara.

Talaka ne wanda zai yi siyasa ta a mutu a kan wani ko a kan jam’iyya amma kuma duk da hakan a yi nasara ya zamo an juya mai baya an dafe madafun iko.

Tabbas an daɗe a nai ma talakawa alƙawura kamar da gaske wanda idan nasara ta zo sai dai su bar ma Allah haƙƙin su. Ina fatan yan siyasa su riqa kyakkyawar kula cewa ba ka zamaninka kuma kai na wasu idan ma an zave ka ko kuma an damka ma ka wani mukami lokaci ne za a zo inda siyasai ta aje ka ta ɗauko wasu inda a nan kuma duk waɗanda kai ma girman kai a cikin talakawan sun zamo abokan tattaunawa.

Dan siyasa ka riƙa amfani da damar ka wajen sauke nauyin jama’a idan ka ki tun a nan duniya za ai nadama domin ba bu abunda ke dauwama.

Talaka a daina siyasa ta a mutu domin ko an kashe ka su a cen gaba za su haɗu wajen amfanar da junansu. Ba a ce kar a yi siyasa ta ra’ayi ba a dai yi mai sannu.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519/08080140820.