Bankin Musulunci zai kashe wa Nijeriya biliyoyin Dala

Daga BASHIR ISAH

Bankin Bunƙasa Musulunci (UDB) ya shirya zai kashe wa Nijeriya biliyoyin Dalar Amurka domin aiwatar da ayyukan cigaban ƙasa.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka ranar Talata.

Ya ce tallafin ɓangare ne na ribar tattaunawar zuba jari da Shugaba Tinubu ya yi da Mataimakin IDB, Dr. Mansur Muhtar, yayin da suka haɗu a Makka, Saudiyya.

A cewar Ajuri, yayin tattaunawar tasu, Tinubu ya ce, “Nijeriya fitila ce da za ta haskaka wa sauran ƙasashen Afirka hanya, kuma da zarar Afirka ta ɗau haske, duniya za ta yi wa al’umma daɗin zama.”

Ya ƙara da cewa, Nijeriya ta bada himma wajen ganin ta kyautata goben matasan ƙasar, tare da cewa zuba jari a Nijeriya zai zama harka mafi riba a faɗin duniya.

Shugaba Tinubu ya ci gaba da cewa, Nijeriya na da giɓi a sassa da dama da suka haɗa tashoshin jirgin ruwa, ɓangaren lantarki, harkokin noma da sauransu, wanda hakan wata dama ce ga masu sha’awar zuba jari a ƙasar.

A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban IDB, Dr. Mansur Muhtar, ya ce ɓangaren hada-hadar kuɗaɗe na duniya na bibiyar harkokin Nijeriya inda ya gano akwai tarin amfani idan aka zuba jari a ƙasar.

Ya ce, Shugaban IDB ya bada sanarwar tanadin Dalar Amurka biliyan $50 daga Arab Coordination Group (ACG) don zuba jari a Afirka.