Tinubu ya yi alhinin rasuwar Samanja

Shugaban Ƙsa Bola Tinubu ya jajanta wa iyalan tsohon Soja, ma’aikacin yaɗa labarai, kuma fitaccen jarumi, Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta wuce yana da shekaru 84.

Shugaban ya bayyana rasuwar fitaccen ɗan wasan a matsayin babban rashi na mutumin da ya bayar da gudunmuwa ga ƙasarsa a duk wata dama da ya samu ta hanyoyi daban-daban.

“Marigayi Pategi dan kishin ƙasa ne da ya zaɓi ya amsa kiran ƙasarsa a lokacin da ta ke buƙatar hidimar sa, shirinsa na talbijin, mai taken Samanja, ya ɗebi ɗimbin shekaru a matsayin bakandamiyar wasan barkwancin da aka yi amfani da shi wajen cusa wa matasa kishin kasa da sanin kimarta da ta masu yi mata hidima. Hakika ya bar abubuwan da ba za a mantawa da su ba,” in ji Shugaban.

Shugaba Tinubu ya yi kira ga iyalan marigayin, da gwamnatocin jihohin Kwara da Kaduna, da Majalisar Masarautar Pategi, da ‘yan wasan kwaikwayo, da ma daukacin yan ƙasa da su yi koyi da halayen marigayin. Ya kuma yi addu’ar samun dangana ga iyalan mamacin.

Shugaban ya bayyana alhininsa kan rasuwar marigayin ne cikin sanarwar da ya fitar mai ɗauke da kwanan wata 14 ga Nuwamba fa sanya hannun kakakinsa, Ajuri Ngelale.