Sojoji sun bayyana sunayen shugabannin ’yan ta’addan da aka kashe a makon jiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Alhamis ne babban kwamandan rundunar sojin ƙasar ya fitar da cikakken bayanan wasu manyan kwamandojin ’yan ta’adda da aka kashe a yankin Arewacin ƙasar nan a yayin gudanar da ayyuka daban-daban a dukkanin wuraren da ke fama da rikici a tsakanin watan Janairu zuwa Maris, 2024.

Daga cikin waɗanda sojojin suka kashe sun haɗa da shugaban lardin Is-Al Furqan (ISGS da ISWAP), Abu Bilal Minuki wanda aka fi sani da Abubakar Mainok a cikin ‘yan ƙungiyarsa masu aikata laifuka da kuma Haruna Isiya Boderi.

An ruwaito cewa, a ranar 21 ga watan Fabrairun 24 ga watan Fabrairu ne sojoji suka kashe Mainok, wani ɗan ta’adda da ya yi ƙaurin suna a dajin Birnin Gwari a Jihar Kaduna da kuma babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar tsaro da ke Abuja, Daraktan ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Edward Buba, ya bayyana cewa sojoji sun kashe Kachallah Damina tare da wani fitaccen ɗan ta’adda Mainok da Boderi a ranar 24 ga Maris.

Ya shaida wa manema labarai cewa an kashe Damina ne tare da mayaƙansa sama da 50 da suka haɗa da Kachallah Alhaji Dayi, Kachallah Idi (Namaidaro), Kachallah Kabiru (Doka), Kachallah Azarailu (Farin-Ruwa), Kachallah Balejo, Ubangida, Alhaji Baldu da dai sauransu.

Buba, Manjo-Janar ya lara da cewa, an kashe ’yan ta’adda 2,351, yayin da aka kama 2,308, sannan kuma an kuvutar da mutane 1,241 da aka yi garkuwa da su, a tsawon lokacin da aka yi garkuwa da su.

“Rundunar soji na yaƙi da muggan maƙiya a ayyukan da suke ci gaba da yi a faɗin ƙasar nan.

Amma duk da haka, sojoji a shirye suke, sun shirya kayan aiki da kuma mai da hankali kan abin da za su yi da waɗannan ’yan ta’adda da maƙarƙashiyar su.

“Tabbas, mun kasance muna tattara bayanan sirri, muna farautar su kuma mun fatattake su a inda za su iya voyewa. Manufarmu ita ce mu kashe daƙile ‘yan ta’adda da waɗanda ke tallafa musu,” inji shi.

Babban jami’in sojan ya bayyana cewa an samu nasarar ne ta hanyar kai hare-hare ta sama da ƙasa a yankunan ’yan ta’adda.