*Ba gudu ba ja da baya, inji jam’iyyar
*Saraki ya nemi a tsahirta
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, tana ci gaba da ninƙaya cikin wutar rikici bayan da kotuna daban-daban ke bayar da mabambantan hukunce-hukunce game da babban taronta na ƙasa.
A ranar Talata wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta sake dakatar da jam’iyyar daga gudanar da babban taronta da take shirin yi a garin Ibadan na jihar Oyo.
Wannan shi ne karo na biyu da kotu ta hana gudanar da taron, wanda babbar jam’iyyar hamayyar ke shirin yi a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.
Sai dai kafin wannan hukuncin na biyu, wata kotun a jihar Oyo ta umarci jam’iyyar da ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta na babban taron, wanda hakan ya haifar da taraddudi.
A wannan shari’a ta baya-baya, tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ne ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar hana shi yin takarar shugabancin jam’iyyar.
Lamiɗo ya shigar da ƙara ne yana buƙatar kotu ta dakatar da jam’iyyar daga zaɓen fitar da sababbin shugabanni.
Wannan shi ne rikici na baya-bayan da PDP ta faɗa a ciki, bayan rikicin shugabanci da ta daɗe tana fama da shi.
A yanzu haka baya ga shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin Iliya Damagun, akwai wani ɓangaren da ke iƙirarin shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Muhammed, wanda har ya kafa wani kwamitin amintattu na daban ƙarƙashin jagorancin Sanata Mao Ohuabunwa.
Babandi Ibrahim Gumel, wanda shi ne shugaban jam’iyyar PDP a jihar Jigawa ya ce dalilin da suka sa ɓangaren Sule Lamiɗo ya yanke shawarar zuwa kotu shi ne saboda ”an gaza samun malaha ta hanyar lalama.”
Ya ƙara da cewa Sule Lamiɗo bai je kotu domin a hana jam’iyyar gudanar da babban taronta ba, sai dai “domin a yi taron yadda ya kamata, ba lallai sai an yi shi a lokacin da aka tsara ba a yanzu.”
A ɗaya ɓangaren, ɗaya daga cikin ginshiƙan jam’iyyar da ke tare da shugaban jam’iyyar Iliya Damagun, Umar Tsauri ya ce lamarin abu ne da ya kamata a warware shi ta hanyar tattaunawa, ba a kotu ba.
Ya ce tuni jam’iyyar ta kafa kwamitin sulhuntawa tsakanin ɓangarorin da ke adawa da juna, amma ba a fara zama ba har zuwa lokacin da kotun ta yanke wannan hukunci.
Umar Tsauri ya ce “zuwa kotu ba ya taimaka wa jam’iyya kuma ɓatanci yake haifarwa”.
Masani kan harkokin siyasa, Farfesa Abubakar Kari, malami a Jami’ar Abuja ya ce “akwai sarƙaƙiya game da halin da jam’iyyar PDP take ciki kuma sai dai a yi hasashe game da makomar jam’iyyar”.
Ya ambato zargin da wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar ke yi na cewa akwai “wasu mutane da suke haddasa husuma a cikin jam’iyyar da gangan domin tabbatar da cewa ba ta taka rawar gani ba a babban zaɓen ƙasar mai zuwa.”
Ya ce “abin da suke yi da gangan ne domin ganin jam’iyyar ta ɓalɓalce, ta rasa girma da kimarta.”
Kari ya ƙara da cewa ba za a iya yin sulhu da irin waɗannan mutane ba.
Sai dai ya bayyana cewa akwai ɓangarorin da ke taƙaddama da shugabancin jam’iyyar waɗanda za a iya sulhuntawa da su.
“Kamar irin su Sule Lamiɗo, ana iya sulhuntawa da su, takara kawai ya ce yana so ya yi, kuma takara ba cin zaɓe ba ne.
“Idan aka dage cewa ba zai yi takara ba, har aka bari ya je kotu, ni ina ganin kamar shugabannin jam’iyyar sun daɓa wa kansu wuƙa ne a ciki.”
A ƙarshe malamin jami’ar ya bayyana cewa babu tabbas game da yiwuwar ficewar PDP daga rikicin da take ciki gabanin babban zaɓe na 2027.
“Akwai waɗanda za a iya sasanta rigimar da ake yi da su, akwai kuma waɗanda sai dai a yi taho mu gama da su,” a cewar Kari.
Masanin siyasar ya yi hasashen cewa idan har aka ƙara nan da wata uku ko huɗu jam’iyyar ba ta magance matsalolinta ba “to ina ganin zaɓukan 2027 sai dai su ji a salansa”.
Ya bayyana cewa ya zuwa watan Afrilu ko Mayun shekara ta 2026 za a fara maganar zaɓukan fitar da gwani, kuma a ƙa’ida shugaba da sakataren jam’iyya ne za su riƙa tura sunayen masu yin takara kuma wajibi ne sai hukumar zaɓe ta halarci tarukan da za a yi.
“To idan ana samun hukunce-hukuncen kotu wadanda za su hana hukumar zaɓe halartar waɗannan taruka da kuma taƙaddama kan ko su wane ne shugabanni na haƙiƙa, ko da sun yi zaɓukan fitar da gwani ba lallai ne a sahhale wa waɗanda suka samu nasara su shiga zaɓe ba,” inji masanin.
Sai dai masanin siyasar ya bayyana cewa PDP ta sha shiga cikin rikita-rikita ta siyasa a baya, amma duk da haka ta sulhunta kuma ta ci gaba da kasancewa jam’iyya mai ƙarfi da kwarjini a faɗin ƙasar.
‘’Wannan ba shi ne karon farko da PDP ta taɓa samun kanta a irin wannan hali ba, duk da cewa a baya rikicin bai kai har gab da zaɓe ba.
“Idan an tuna bayan faɗuwa zaɓe a 2015, jam’iyyar ta faɗa cikin rikicin shugabanci har ta samu shugabanni biyu – Ali Modu Sharif da Ahmed Makarfi – har sai da aka kai Kotun ƙoli.”
Ya bayyana cewa har yanzu PDP na da ƙarfi, da ɗimbin magoya baya da kuma tsari a kowane yanki na ƙasar nan, “sai dai abin da ke faruwa a cikinta na mata illa sosai, kuma hakan na rage mata girma da ƙima.”
Za mu yi taronmu ba gudu ba ja da baya, inji jam’iyyar
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana ƙudurinta na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na ƙasa da aka tsara a yi a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba.
Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa Manhaja cewa hukuncin kotun da ke dakatar da taron “ɓata lokaci ne kawai,” yana mai jaddada cewa jam’iyyar na bin hukuncin da Kotun ƙoli ta yanke a baya wanda ke tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa suna da ikon gudanar da harkokinsu na cikin gida ba tare da tsoma bakin kotu ba.
Wannan bayani na Abdullahi ya biyo bayan hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu na Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke a ranar Talata, inda ya hana PDP gudanar da taronta.
A martaninsa ranar Talata, Abdullahi ya ce PDP ba za ta sake yarda da “hukuncin da aka samo da gangan” ba, yana mai cewa jam’iyyar PDP ‘yan Nijeriya ne suka kafa, ba kotu ba.
“Hukuncin ɓata lokaci ne. Mun yi nisa sosai da ba za a iya dakatar da mu ba,” inji shi.
“Ba kotu ce ta kafa mu ba, ‘yan Nijeriya ne suka kafa mu, kuma su ne ya kamata mu saurara, ba hukuncin da aka samo da gangan ba.
“Ba za su iya dakatar da mu ba. Muna da hukuncin kotun ƙoli da ke cewa harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa suna ƙarƙashin ikon su ne kawai, kuma muna bin wannan doka. Ko da wani ya yi watsi da hukuncin Kotun Jihar Oyo da ta ba mu damar ci gaba, ba zai iya watsi da hukuncin kotun ƙoli ba. Ba za mu ci gaba da bin saɓanin hukuncin kotuna ba. Mun yi nisa sosai; ba za a dakatar da mu ba.
“Su jira sai bayan mun kammala, sai su gwada ƙin amincewa da shi, idan za su iya. Duk da haka, suna da damar ɗaukaka ƙara, amma mu mun yi gaba,” inji shi.
A gefe guda kuma, tuni mambobin Kwamitin Shirya Babban Taron ƙasa na PDP (NCOC) sun kai ziyara Ibadan a ranar Talata domin duba wurin da za a gudanar da taron.
Mataimakin Gwamnan Jihar Oyo, Barista Bayo Lawal, wanda ke shugabantar kwamitin wurin taron na Babban Taron PDP na 2025, ne ya jagoranci duba wurin a Filin Wasa na Lekan Salami.
Kwamitin ya kuma gudanar da taro da masu kula da filin wasan da ‘yan kwangila domin kammala shirye-shiryen kayan aiki kafin taron da ake sa ran yi a ranar Asabar mai zuwa.
Saraki ya shawarci jam’iyyar ta dakatar da taron
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya Bukola Saraki ya shawarci jam’iyyarsu ta PDP mai adawa ta dakatar da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa a jihar Oyo saboda umarnin kotuna kan hakan.
Saraki ya bayar da shawarar cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na dandalin ɗ ranar Laraba bayan wata ganawa da kwamatin sasanta ‘ya’yan jam’iyyar ƙarƙashin jagoracin Hassan Adamu.
Tsohon shugaban da ya jagoranci majalisa daga 2015 zuwa 2019 ya ce umarnin kotuna kusan huɗu masu karo da juna game da babban taron zai iya jawo matsala game da halaccin duk wani mataki da ya biyo bayan taron.
Zuwa yanzu, akwai ƙararraki uku a gaban kotuna daban-daban waɗanda suka bayar da umarnin a dakata da shirin taron da kuma akasin haka.
Ministan Abuja Nyesom Wike, da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido na cikin waɗanda suka kai jam’iyyar kotu kan taron.
Yanzu dai za mu gani, gobe Asabar PDP za ta gudanar da taron kamar yadda jam’iyyar ta yi alwashi ko a’a.
