Tasirin motsa jiki ga lafiya (2)

Daga AISHA ASAS

Motsa jiki na ƙara yawan jinin da ke isa ƙwaƙwalwa:

Yayin da ka ke motsa jiki, ɗan aike da ke kai saƙon jiki zuwa ƙwaƙwalwa zai ƙara girma, don haka zai kai jikin wadatacce. Haka zalika, zai iya tasiri wurin halittar wasu ƙwayoyin halitta da ke da matuƙar muhimmanci a lafiyar ƙwaƙwalwa.

Motsa jiki na taimakon matsalar ciwon ƙafa da hannu:

Duk da cewa, an fi ɗora alhakin matsalar ciwon ƙafafu ko hannaye a ƙarancin gishiri a jikin ɗan Adam, wannan ce ke sa, matsalar ta fi yawaita a lokacin zafi, kasancewar yawan zufa da ake yi.

Da wannan wasu ke ganin jikin mai fama da matsalar yawan ciwon ƙafa ko hannu (idan ka cire masu matsalar kariyya da makamantansu) ya fi buƙatar yawaita cin gishiri (masu cutukan da ke da matsala da gishiri kamar hawan jini kada ku haye da yawa, zai fi ku fara da tuntuɓar likitansu kafin ku san adadin da ya kamata ku ci, wanda ba zai yi sanadin motsa ciwon ba.)

Duk da haka, motsa jiki na da rawa babba da yake takawa wurin samar da lafiya ga matsalar, idan ka lura da cewa, shi kansa rashin motsa jikin na haifar da ciwon gaɓoɓi ciki har da ƙafa da hannuwa.

Baya ga haka, akwai matsaloli irin na ciwon magamar gaɓoɓi kamar gwiwa da sauransu, masana sun faɗa cewa, qafewar ruwan da ke ba wa wurin damar lanƙwasawa ba tare da matsala ba ce ke haifar da wannan ciwo, domin gaɓar zata haɗu da ‘yar’uwarta, waɗanda dukkansu suka kasance qashi, haɗuwar ta su kuwa dole su yi zafi.

Daga cikin mafita daga matsalar da masana suka faɗa bayan ababen da za su yi don dawowar ruwan, akwai motsa jiki, wanda suka ce tun farko rashin sa na ɗaya daga cikin ummul khaba’isin matsalar.

Idan aka yi duba da lokacin da wannan matsalar ta fi yawaita, wato lokacin sanyi, za mu gane motsa jiki bai cika samuwa ba a lokutan sanyi.