Yadda ɗan ƙwallon ƙafa, Hakimi ya tserar da dukiyarsa yayin da matarsa ta nemi a raba aurensu

*Ta shigar da ƙara a ba ta rabin dukiyarsa
*Da sunan mahaifiyarsa ya yi wa komai nasa rijista
*Yanzu matar ce za ta ba shi rabin dukiyarta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rabuwar auren Hiba Abouk ’yar shekraru 36 da shahararren ɗan wasan Moroko Achraf Hakimi mai shekaru 24, ya bazu a kafofin sada zumunta, bayan da aka ruwaito cewa matar ta shigar da ƙara kan ɗan wasan na Paris Saint-Germain da ya sake ta kuma a ba ta rabin dukiyarsa.

Hakimi na fuskatar tuhuma bisa zargin yi wa wata yarinya fyaɗe, lokacin da matarsa tare da ’ya’yansu da kuma mahaifiyarsa suka yi balagurio zuwa Dubai.

An ruwaito cewa, Hiba na neman rabin kadarorin da Hakimi ya mallaka, amma ta yi mamaki da ta samu labarin cewa ba shi ko ƙarfanfana a sunansa.

Hakan na nufin Hiba ba za ta karɓi wani ɓangare na dukiyar tsohon mijin na ta ba

Wanda ke cin gajiyar albashi da dukiyar Hakimi ba kowa ba ne illa mahaifiyarsa wadda ta shafe shekaru da dama tana karɓar albashinsa a asusun bankinta.

Duk da cewa wannan labari ya ya janyo hankali sosai a ƙasashen Sifaniya, Faransa da kuma Moroko, duk kuwa da cewa Hiba ba ta cikin wani hali da ta ke buƙatar wani ɓangare na dukiyar tsohon mijin nata domin samun damar taimaka wa rayuwa, la’akari da cewa itama tana da tata dukiyar mai tarin yawa, amma abin mamakin shi ne yadda ta nemi a ba ta rabin dukiyar tsohon mijin na ta.

Al’umma da dama daga sassan duniya, na jinjina wa ɗan wasan, musamman yadda ya nuna ƙauna ga mahaifiyarsa, da kuma kaucewa faɗa wa irin wannan sarƙaƙiya da mata ke yi a ƙasashen Turai, da kuma la’akari da yadda matan ‘yan ƙwallo da dama kan nemi maƙudan kuɗaɗe idan suka nemi rabuwa da su.

Sai dai a wasu wuraren kuma, ɗan wasan ya sha suka, inda wasu ke ganin bai kamata ya miƙa ragamar dukiyar tasa kacokaf ga asusun mahaifiyar tasa ba.