Yadda ’yar Nijeriya, Tobi Amusan ta kafa tahiri a gasar tseren duniya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

  • Tobi ’yar gaban goshin Nijeriya ce – Buhari
  • Yadda nasarar ta sa ’yan Nijeriya zubar da hawayen farin ciki
  • Kocin Super Eagles ya yaba wa Tobi da Brume
  • Afirika na alfahari da Tobi – Usain Bolt
  • Shugaban Hukumar AFN ya taya ta murna

‘Yan Nijeriya sun yi matuƙar farin cikin ganin yadda Tobi Amusan, ‘yar shekara 25, haifaffiyar garin Ijebu Ode na Jihar Ogun, ta zama ‘yar wasan Nijeriya ta farko da ta lashe kofin zinare a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, bayan da ta samu nasara a gasar tseren mita 100 na mata a Oregon da ke ƙasar Amurka a ranar Lahadi, 17 ga Yuli, 2022.

Ba wai kawai ta ci zinare ba amma ta shafe tarihin duniya a wasan kusa da na ƙarshe na ban mamaki inda ta ci kan daƙiƙa 12.12 a filin Hayward a daƙiƙa 12.06.

An haifi Oluwatobiloba Ayomide, wacce ake kira da ‘Tobi’ Amusan, Tobi Amusan (kamar yadda ake kowa ya ke kiranta) an haife ta ne a ranar 23 ga Afrilu 1997. Zuwa ranar haihuwarta, a halin yanzu tana da shekaru 25 kenan.

‘Yar wasan tseren ce ta Nijeriya wacce ta kware a tseren mita 100 sannan kuma tana fafatawa a matsayin ‘yar tsere.

‘Yar Nijeriya Tobi Amusan ta lashe kyautar zinariya a gasar mita 100 ta tseren mata ta Duniya da ake gudanarwa a Amurka.

‘Yar wasan mai shekara 25 ta kafa tarihin ne a zagayen kusa da ƙarshe inda ta kai layi cikin minti 12 da daƙiƙa 12.

A baya dai Ba’amurkiya Kendra Harrison ta kafa irin wannan tarihi a 2016 inda ta kai layi a minti 12 da daƙiƙa 20.

Amusan ta fi yin gudu a zagayen ƙarshe (ta yi minti 12 da daƙiƙa shida), amma ba a amince da nasararta ba saboda iska mai ƙarfi da ke ƙara mata gudu.

Tobi ta zubar da hawaye don jin daɗi a yayin da ake buga taken Nijeriya a filin wasa na Hayward Field, Eugene da ke Jihar Oregon, saboda bajintar da ta yi wa ƙasarta.

‘Yar ƙasar Jamaica Britany Anderson ta lashe kyautar azurfa yayin da ‘yar ƙasar Puerto Rico wadda ita ce gwarzuwar gasar Olympic Jasmine Camacho-Quinn ta lashe kyautar tagulla.

Yayin da ta ke bayani bayan ta samu nasara, Tobi ta ce, “na yarda da kwazotakata amma ban taɓa tsammanin zan kafa tarihi a duniya ba.”

’Yan Nijeriya da dama sun yi ta zubar da hawayen farin ciki ganin yadda ’yar ƙasarsu ta kafa tarihin da ba a taɓa kafawa ba a faɗin nahiyar Afirika.

Mutane ne dai sun yi ta fitowa a kafafen sada zumunta domin nuna farin cikinsu da kuma alfaharinsu da ’yar ƙasarsu.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya taya Tobi Amusan murnar lashe kofin zinare na tsaren mita 100 na mata a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta 2022, inda ta kafa sabon tarihi a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a gasar wasannin motsa jiki da kuma zama ’yar Nijeriya ta farko da ta taɓa lashe gasar kofin duniya.

Shugaban ya bi sahun miliyoyin ’yan Nijeriya wajen murnar wannan gagarumin bajinta da ’yar ƙasarta kuma ta taɓa zama zakara a gasar cin kofin Afrika sau biyu, wadda a dare ɗaya ta baiwa duniyar wasanni mamaki da bajintar da ta taka.

Ya godewa fitacciyar ’yar wasan kan rera waƙar taken ƙasar Nijeriya daga dandalin qasa da ƙasa, wanda ya bar al’ummar ƙasar cikin nishaɗi da kuma abubuwan da ba za a manta da su ba na hawayen murna da nasara; bege da nasara da aminci.

Shugaban ya ce, fitacciyar sana’a da nasarorin da yarinyar ta samu za ta ci gaba da zaburar da ‘yan wasan Nijeriya masu tasowa don samun gagarumar nasara.

Shugaban ya kuma yabawa Ese Brume da ta wakilci Nijeriya cikin girmamawa da alfahari, inda ta samu lambar azurfa a gasar tsalle-tsalle ta mata.

Ya yaba wa ƙungiyar ta Nijeriya bisa nuna jajircewa da gaskiya da kuma kyakykyawan wasannin motsa jiki a fagen wasanni a duniya, inda ya tabbatar da cewa tare da aiki tuƙuru da jajircewa, ana iya samun nasara.

Tobi ta zubar da hawaye don jin daɗi a yayin da ake buga taken Nijeriya a filin wasa na Hayward Field, Eugene da ke Jihar Oregon, saboda bajintar da ta yi wa ƙasarta.

Kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya yabawa ‘yan wasan biyu, Tobi Amusan da Ese Brume saboda rawar da suka taka a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta 2022.

Mutumin da ya fi gudun tsere a duniya, Usain Bolt, a ranar Litinin ya taya fitacciyar ’yar wasan Nijeriya, Tobi Amusan, murnar kafa tarihi a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka kammala.

Shugaban hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Nijeriya (AFN), Cif Tonobok Okowa, shi ma a safiyar Litinin, ya taya budurwar zinare, Tobi Amusan da ’yar wasan ƙasar, Ese Brume, murnar kammala gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka kammala a shekarar 2022, a jihar Oregon ta Amurka.