‘Yan bindiga sun kashe Kanal ɗin sojin Nijeriya yayin ƙoƙarin hana su sace shi da iyalansa a Abuja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani Kanal mai aiki a sashen leƙen asirin Sojin Nijeriya, Abdussalam Ude, ya rasu bayan da wasu ‘yan bindiga suka harbe shi yayin da yake ƙoƙarin hana su sace shi a gidansa da ke unguwar Kurudu a Abuja.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, jim kaɗan bayan jami’in ya dawo gida. A cewar PRNigeria, maharan sun buɗe masa wuta ne yayin da yake fitowa daga motarsa, kafin su yi ƙoƙarin yin garkuwa da shi.

Sai dai Mista Ude, wanda Kanal ne a rundunar sojin Nijeriya, ya yi ƙoƙarin kare kansa duk da cewa maharan sun fi shi yawa. Rahotannin tsaro sun ce hakan ya hana maharan cimma burinsu na yin garkuwa da shi, amma daga bisani suka harbe shi har sau da dama, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Harin ya kuma jikkata matarsa, direbansa da wani jami’in tsaro da ke gidansa, inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan lamarin. Da PREMIUM TIMES ta tuntubi mai magana da yawun rundunar, Appolonia Anele, ta ce za ta dawo da bayani daga baya.

Unguwar Kurudu da ke wajen birnin Abuja na ɗaya daga cikin wuraren da jami’an soja da iyalansu da dama ke zaune, musamman a gidajen mallakar rundunar.

A ‘yan shekarun nan, an samu ƙaruwar hare-haren masu garkuwa da mutane a wasu yankunan da ke bayan gari a Abuja, duk da cewa jami’an tsaro sun yi nasarar kama wasu da ake zargi da aikata irin waɗannan laifuka.

Rahoton PRNigeria ya ce marigayin ya taɓa riƙe muƙamai masu muhimmanci a fannin leƙen asiri da yaƙi da ta’addanci a rundunar soji. Haka kuma ya halarci ayyukan yaƙi da ‘yan tada ƙayar baya a Arewa maso Gabashin Nijeriya, tare da gudanar da wasu ayyuka na musamman a ƙasashen Chadi da Faransa.

Ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka kai harin da kuma cafke su.

Marigayin, wanda ya fito daga Jihar Enugu, ana sa ran za a ɗaga matsayinsa zuwa Birgediya Janar a shekara mai zuwa. An shirya yi masa jana’iza ranar Talata a Masallacin Mambilla da ke Abuja bisa tsarin addinin Musulunci.

By ukarofi