‘Yan Majalisar Wakilai huɗu daga Zamfara sun koma APC

Daga Sanusi Muhammad, a Gusau

Wasu ‘yan Majalisar Wakilai su huɗu daga jihar Zamfara sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

‘Yan majalisar sun bayyana sauya sheƙar nasu a hakumance ne yayin zaman majalisar a yau Talata a Abuja.

Waɗanda lamarin ya shafa su ne; Bello Shinkafi mai wakiltar Shinkafi/Zurmi; Ahmed Bakura mai wakiltar Bakura/Maradun; Ahmed Shehu mai wakiltar Bungudu/Maru; da kuma Suleiman Gummi mai wkiltar Gummi/Bukkuyum.

An ji Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya karanto wasiƙar ‘yan majalisar ta barin PDP zuwa APC a lokacin zaman majalisar.

Idan dai ba a manta ba, Manhaja ta rawaito yadda Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya sauya sheƙa inda ya bar PDP ya koma APC a Talatar makon jiya.

Ya zuwa yanzu, ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara su 24 da sanatocin jihar su uku haɗa da ‘yan majalisar wakilai shida daga cikin bakwai da jihar ke da su, duk sun bi sawun Matawalle zuwa APC.

Sai dai har yanzu Mataimakin Gwamnan Jihar, Aliyu Gusau, tare da ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Anka/Talata-Mafara, Kabiru Mafara, na ci gaba da zamansu a PDP.