‘Yan sanda a Kano sun damƙe wanda ya yi yunƙurin kuɓutar da mai garkuwa

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani mai Suna Alhaji Bawa ɗan asalin Shika a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna bisa zargin bai wa ɗan sanda, SP Aliyu Mohammed, da ke Sashen Binciken Manyan Laifuffuka cin hancin naira milyan ɗaya (1,000,000:00) don ya saki wani mai garkuwa da mutane.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce, wanda aka yi yunƙurin kuɓutar da shi ɗin mai suna Yusuf Ibrahim, ɗan asalin Garin Danjibga da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe, Jihar Zamfara an kama shi ne a tashar motar Rijiyar Zaki da ke Jihar Kano bisa zargin garkuwa da mutane.

Sanarwar ta ƙara da cewa, jami’an samar da zaman lafiya ƙarƙashin jagorancin CSP Usman Abdullahi DPO na yankin Rijiyar Zaki suka samu nasarar kama shi bayan an bayyana shi ta hanyar wani direban mota da suka yi garkuwa da shi a hanyar Funtua zuwa Gusau, inda suka karɓi Naira 500,000 a matsayin fansa kafin su sako shi.

Haka kuma, sanarwar ta ce a yayin da aka tsaurara bincike wanda ake zargin ya amsa laifinsa, ya ce yana cikin waɗanda suke garkuwa da mutane tsakanin garuruwan Sheme da Yankara da Faskari da garin Kucheri dake jihohin Katsina da Zamfara, inda ya yi iƙirarin ƙungiyarsu ta kashe mutum 10, daga ciki ya kashe biyu da hannunsa.

Kawo yanzu an miƙa batun ga kotu don zurfafa bincike.

Wakilinmu ya rawaito Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Mamman Dauda, ya yaba dangane da haɗin kan da al’ummar Kano ke bai wa jami’ansu a bakin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *