Zaɓen 2023: Gwamnati ta rufe kwalejojin fasaha

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe duka kwalejojin fasaha da ke faɗin ƙasa har sai bayan babban zaɓe mai zuwa.

Wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan da Gwamnati ta ba da umarnin rufe ɗaukacin jami’o’in da ke faɗin ƙasar.

Umarnin rufe makarantun na ƙunshe ne cikin takardar sanarwar da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta aike wa hukumomi da shugabannin makarantun da lamarin ya shafa ta hannun Hukumar NBTE

Wasiƙar, wadda Mr I. O Folorunsho ya rattaɓa wa hannu a madadin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, mai ɗauke da kwanan wata 10 ga Fabrairu, an raba ta ga manema labarai ranar Litinin a Abuja.

“Bisa la’akari da tsaron ma’aikata da ɗalibai da dukiyar makarantunmu, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya ba da umarnin rufe duka kwalejojin fasaha da ke faɗin ƙasa bayan tuntuɓar hukumomin tsaron da lamarin ya shafa.

“An dakatar da harkokin karatu daga ranar Laraba, 22 ga Fabrairu zuwa Talata, 14 ga Maris 2023,” in ji wasiƙar.