Sanƙarau ta kashe mutum 20 a Jigawa

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce cutar Sanƙarau ta kashe mutum 20 a faɗin jihar, lamarin da ya ɗaga hankalin jama’a da hukumomi a jihar.

A cewar Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Dr. Salisu Mu’azu, mutum 80 aka tabbatar da sun kamu da cutar daga cikin 360 da ake zargi, sannan ana fargabar ta kashe mutum 20 tun bayan ɓullarta a jihar.

Sanarwar da Sakataren ya fitar ta ce, “Cikin alhini muke sanar da ɓullar cutar sanƙarau a Jihar Jigawa.

“Mun tabbatar mutum 80 sun kamu da cutar, sannan ta yi ajalin mutum 20,” in ji Mu’azu.

Jami’in ya ba da tabbacin gwamnatin jihar na yin dukkan mai yiwuwa tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen yaƙi da cutar.

Ya ce, “Muna kira ga al’ummar Jihar Jigawa kowa ya ɗauki matakin kare kansa da iyalansa daga barin kanuwa da cutar.”

Manhaja ta rawaito Shugaban Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC), Dr Ifedayo Adetifa, ya ce hukumar ta yi taron gaggawa da Gwamnatin Jigawa kan ɓarkewar cutar a jihar da kuma yadda za a shawo kanta.