Dalilin soke taron Atiku a Ribas – PDP

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP a Jihar Ribas, ya ce an soke gangamin kamfe na Atiku Abubakar da aka shirya gudanarwa a Fatakwal don kauce wa asarar rayuka.

Shugaban Kwamitin a Jihar Ribas, Sanata Lee Maeba ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya shirya ranar Litinin a Fatakwal, babban birnin jihar.

Maeba ya ce an kai wa mambobin PDP da magoya bayan Atiku hare-hare a tsakanin watanni ukun da suka gabata a jihar.

Kazalika, ya yi zargin Gwamnatin Ribas ta rufe harkokin kasuwancin wasu jiga-jigan mambobin jam’iyyar masu mara wa takarar Atiku baya a jihar.

Ya ƙara da cewa, a Disamban da ya gabata an kashe shugaban ɓangaren matasa na kwamitin kamfe ɗin Atiku/Okowa, Rhino Owhohaire, a ƙauyen Alu da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ikwerre a jihar.

“Duk da an kama wanda ake zargi, amma Gwamnatin Jihar Ribas ta karɓi belinsa,” in ji Maeba.

Ya ƙara da cewa, ko a ranar 5 ga Fabrairun 2023, an kama wasu magoya bayan Atiku su 31 yayin da suke tsaka da tattaunawa a Fatakwal inda aka tisa ƙeyarsu zuwa kurku ba bisa ƙai’da ba.