Daga AISHA ASAS
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta bayyana damuwarta dangane da yadda akan biya kuɗaɗen fansa wajen kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su a hannun ‘yan bindiga.
Ƙungiyar ta bayyana damuwarta ne a wani bayanin da Sakatarenta na Hulɗa da Jama’a na Ƙasa, Emmanuel Yawe, ya fitar Asabar da ta gabata a Kaduna.
ACF ta yi amfani da wannan dama wajen jinjina wa duka waɗanda suka sadaukar da ransu wajen tattaunawa da ‘yan fashin dajin domin kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su, musamman ma ɗaliban Jami’ar Greenfield, Kaduna.
Ta ce “Mun gode wa Allah da ya kuɓutar da su ya kuma sake sada su da ahalinsu, ‘yan’uwa da kuma abokan arzikk na kusa da nesa.”
Yawe ya ce nadamrsu guda ita ce, “Yadda aka kwashi milyoyin Naira aka bai wa ‘yan fashin kafin kuɓutar da daliban.”
Ya ci gaba da cewa a matsayinsu na ƙungiya ba su yarda da batun kuɗin fansar da aka biya ‘yan ta’addan ba, amma suna goyon bayan zaman tattaunawa da su.
Daga nan, ACF ta yi magiya ga ‘yan fashin da su duba sannan su saki sauran mutanen da ke hannunsu baki ɗaya ba tare da wani jinkiri ba. Tana mai cewa ko ma dai mene ne fushinsu, zubar da jinin jama’a ba shi ne mafita ba.