Ɗan sane ya sace wayar Kalu yana tsaka da karɓar takardar shaidar cin zaɓe a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wasu masu sane da ba a san ko su waye ba sun sace wayar Sanata mai wakiltar mazaɓar Abiya ta Arewa, Orji Uzor Kalu, a lokacin da ya je karɓar takardar shaidar lashe zaɓe a ɗakin taro na International Conference Centre a Abuja.

Sanatan ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa ta shafinsa na Facebook da aka tabbatar a ranar Alhamis, 9 ga Maris, 2023.

Tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana cewa, wayar salular da wani wanda har yanzu ba a tantance ba ya sace na ɗauke da layukansa na MTN da Glo.

Ya kuma gargaɗi jama’a da su yi hattara da duk damfara da a ya shafi wayarsa da lambobinsa.

“Wannan shine don sanar da jama’a da su yi hattara da duk wani saƙo da ya shafi wayar salula da lambobina. Yayin da ake karɓar takardar shedar dawowa a International Conference Centre Abuja, wani da ba a tantance ba ya sace wayar salulata mai ɗauke da layukan MTN da Glo.

“An sanar da masu samar da hanyar sadarwa ta yadda ya kamata. Don Allah kar a yi jinkirin samar da kowane bayani mai amfani,” Kalu ya rubuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *