2023: An buga gangar siyasa

Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA

Akwai jihohi 36 a Nijeriya, akwai kuma Birnin Tarayya a Abuja. Akwai ƙananan hukumomi 774. Akwai mazavu dubu takwas da ɗari takwas da 12. Akwai akwatunan zave dubu 176 da 846. Akwai mutum miliyan 96 da dubu 200 waɗanda suka mallaki katin zaɓe. Akwai jam’iyyu 18 da suka tsayar da yan takarar shugabancin Nijeriya a zaɓen da za a yi ranar 25 ga watan Fabrairu 2023.

A bisa doron tsarin mulkin Nijeriya na 1979 da 1989 da 1999 wanda duk zai zama shugaban ƙasar Nijeriya sai kashi 25 na waɗanda za su yi zaɓe a jihohi 24 sun zaɓe shi. Dole sai an zave ka a ƙasar Yarabawa a jihohinsu shida. Haka sai an zaɓe ka a jihohin Inyamurai guda biyar.

Haka sai mutanen Neja Delta da suke da jihohi shida sun zaɓe ka. Sai ka samu nasara a jihohin Arewa maso Yamma na asalin Fulani da Hausa guda bakwai.

A arewan kuma sai ka samu gagarumin rinjaye a jihohin Bauchi da Adamawa da Gombe da Borno da Yobe da Taraba, jihohin da suka fi kowane yanki a Najeriya ƙananan ƙabilu da mabanbantan addini. Haka sai ka yi nasara a jihohin Arewa ta tsakiya guda shida.

A halin da ake ciki, jam’iyyar APC da PDP da APGA su ne suke da gwamnoni 36. PDP tana da gwamna 13, APC tana da gwamnoni 22, jam’iyyar APGA tana da gwamna ɗaya a jihar Anambra ƙarƙashin Farfesa Charles Soludo.

Akwai gwamnonin PDP a Arewa guda biyar su ne, Sakkwato da Bauchi da Biniwai da Taraba da Adamawa. Akwai gwamnonin APC a arewa guda 14. A kudancin Najeriya akwai gwamnonin APC guda hudu a yankin Yarbawa Lagos da Ekiti da Ogun da Ondo.

A yankin Inyamurai akwai, Ebonyi da Imo; a yankin Neja akwai gwamnan jihar Kurosribas, Ben Ayade; sauran duk na PDP ne, sai Anambra ta APGA.

A wannan shekarar ne cikin shekara 23 manyan ‘yan takarar da suka fito babu soja sai farar hula. Bola Tinubu da Atiku Abubakar da Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi dukkansu tsabar ‘yan siyasa ne.

Mutum 4 da suke rufa musu baya duka ‘yan siyasa ne. Kashim Shettima na APC, Okowa na PDP, Datti Baba-Ahmed na LP, Rabaran Isac Idahosa na NNPP shi ne kaɗai bare a cikinsu. A wannan zaɓen, akwai Inyamurai suna da jam’iyya tasu LP, Fulani da Hausa suna da Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso, Yarabawa suna da Bola Ahmed Tinubu.

Manyan masu takara guda uku duk Musulmi ne. Duka su huɗun kuma sun tava zama zaɓaɓɓun masu riƙe da muƙamin Nijeriya ko a jiha ko a tarayya.

Cikin masu takara guda huɗu, Atiku Abubakar shi ne ya fi kowanne zaman cikin shiri. Dalili kuwa shi ne, ya fitar da sunan mai rufa masa baya da wuri. Ya fitar da manhajar da zai ɗora manufofinsa a kanta a fili, da yadda za a kai ga aiwatar wa idan an yi nasara.

Ya gabatar da tattaunawa ta musamman da ‘yan kasuwa da masana tattalin arziki a ƙasa, matsalar da ta shafi kowane ɗan Nijeriya, ya kawo tunanin yadda zai tunkare ta. Ya ƙaddamar da babban kwamitinsa na kamfe a kan lokaci, har sun fara aiki kuma an riga ma an fara yawon kamfe.

Da jam’iyyar APC da PDP suna da tangarɗar cikin gida a junansu. Rikicin PDP kowa ya san shi. Na APC a ƙudundune yake. Da jam’iyyar LP da NNPP ko shugabancin kamfen dinsu ba a sani ba, ballantana a ga yadda suka tsara fita don yi wa jama’a bayanai na a zaɓe su.

Ɗan takarar APC yana ta zarya a tsakanin Paris da London da Turai. Shi kuma ɗan takarar NNPP yana kan aikin sanarwa mutanen Najeriya sunan jam’iyyarsa da kuma inda ofishin ta yake na jihohi da ƙananan hukumomi da mazaɓu. Shi kuwa Peter Obi a shafukan Tiwita yana sharafinsa. Kuma har manyan jaridun Duniya irin su Bloomberg sun bashi kofin ya ci zaɓe.

In har kana neman ɗan takarar shugabancin Nijeriya mai tsantsar ƙabilancin yanki, to Bola Ahmed Tinubu ne! Idan kana neman ɗan takarar masu jin haushin Nijeriya kuma, ka nemi Peter Obi na LP.

Idan kana son ganin ɗan takara gwanin tada qura, Rabi’u Musa Kwankwaso ne! Idan kana son ganin ɗan takarar shugabancin Nijeriya kuma ɗan Nijeriya, nemi Atiku Abubakar! A shekarar 1979 jam’iyyar da ta ci zaɓe ita ce wacce ta tsakuro ƙuri’a daga kowanne ɓangaren Nijeriya, wannan jam’iyya ita ce, NPN.

SDP ma ta ci zaɓe a 1993 saboda ta haɗa Nijeriya wuri guda. A shekarar 1999 jam’iyyar PDP ta kafa mulki ne saboda ita ce jam’iyyar Nijeriya. A shekarar 2015, APC ta kafa mulki ne saboda PDP ta yi wa mutanen Najeriya laifi, irin wannan laifin yau APC ta aikata shi. Sakamakon iri ɗaya ya dace a aiwatar shi ne, zaman lafiyar ƙasarmu.

Muhammad Bello Sharaɗa, ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi.