2023: Mun shiga shekarar zaɓe

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A kwana a tashi ba wuya ko kuma a wani kaulin bai bar komai ba. Ma’ana duk abun da a ka sakawa lokaci to in Allah ya yarda zai zo. A Nijeriya a kan gudanar da babban zaɓe ne bayan shekaru huɗu kuma duk wanda ya samu damar ɗarewa kujerar zartarwa ta gwamna ko shugaban ƙasa to zai zauna na tsawon shekaru huɗu a kan karaga sannan ya sake samun damar sake tsayawa in har ya sake lashe zaɓe ya sake yin shekaru huɗu kan kujera daga nan kuma shikenan wannan damar ta kare.

Duk da haka a kan samu wasu dalilai da kan dakatar da wasu daga waɗanda ke kan kujera kammala wa’adi kamar misalin tsigewa daga majalisa, mutuwa ko kuma abun da ba za a ce ya na yiwuwa ba a Nijeriya wato mutum ya yi murabus don tsira da mutunci ko don aikata wani aiki da ya saɓawa muradun jama’a.

Akwai wani dalilin na daban da ya shafi yanke shari’a a kotu kamar abun da ya faru da tsohon gwamnan Ribas Celestine Omehia da kotu ta kwabe Rotimi Amaechi ya dare karaga. Ga ma Emeka Ihedioha a Imo da Kotun Ƙoli ta kwabe Hope Uzodinma ya hau mulki.

Za mu ga misalin barin kujera ta hanyar tsigewa ga tsohon gwamnan Adamawa Murtala Nyako da hakan ya yi sanadiyyar ɗora Umaru Fintiri kan mulki. Ga mataimakan gwamna, ba za mu manta yadda a ka samu saɓani tsakanin tsohon gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda da mataimakinsa marigayi Alhaji Garba Gadi ba.

Hakan ya sa majalisa ta tsige Gadi duk da daga bisani kotu ta dawo da shi kuma sabanin kusan iri ɗaya ne da abun da ya faru a Zamfara inda gwamna Bello Matawalle ya yi wuf ya koma jam’iyyar APC amma tsohon mataimakinsa Mahdi Aliyu ya zauna a PDP don ya na ganin ita ta taimaka ya sha Inuwar ta ya zama mataimakin gwamna.

An tura caji majalisa inda ta tsige shi a ka ɗauko dan Majalisar Dattawa, Sanata Hassan Nasiha Gusau aka ba shi muƙamin. Ga misalai nan Barjak na yanda siyasar Nijeriya ke gudana ta yadda ba wani abu mai wuya ba ne wannan ya ƙaura can wancan ya dawo da nan.

‘Yan ƙalilan ne a tsakanin ‘yan siyasar Nijeriya daga dawowa dimokraɗiyyar nan a 1999 ba su sauya sheqa ba. Wani ma ya sauya sheƙar ya fi sau ɗaya. Hatta shugaba Muhammadu Buhari ya sauya sheƙa a wani tsari na fita daga jam’iyya ya kafa ta sa jam’iyyar.

Shugaban wanda ya yi takara a inuwar ANPP a 2003 da 2007 ya fita daga jam’iyyar ya kafa jam’iyyar CPC wacce ya yi takara a cikin ta a zaɓen 2011 inda gabanin zaɓen da ya lashe a 2015 ya shiga yarjejeniyar haɗe jam’iyyar ta sa da wasu jam’iyyu musamman AC da ita kan ta tsohuwar jam’iyyar ta sa ANPP su ka kafa wannan jam’iyya mai mulki wato APC.

Wani abun dubawa an samu wasu gaggan ‘yan jam’iyya mai mulki a wancan lokacin da su ka shigo gamayyar da sunan sabuwar PDP. Irin waɗannan mutanen sun haɗa da tsohon shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, Sanata Muhammad Danjuma Goje da ma gwamnoni irin su Rabi’u Musa Kwankwaso, Abdulfatah Ahmed, Aliyu Magatakarda Wamakko da sauransu.

Yanzu dai an shiga shekarar da za a gudanar da babban zave a Nijeriya wanda shi ne irin sa na 7 tun 1999 kuma ya samar da shugabanni huɗu kuma cikin su za a ce biyu ne su ka samu shekaru 8 kan mulki kuma wani abun dace sun kuma taɓa jagorantar Nijeriya a matsayin shugabannin mulkin soja wato tsohon shugaba Obasanjo da shugaba Buhari da ke karaga.

Wannan karo ya zama tamkar kowace ƙabila ta samu fito da dan takara mai ƙarfi aƙalla daga yankinta. Ina maganar manyan ƙabilu uku na Nijeriya. Ya na da matuƙar muhimmanci ‘yan Nijeriya su fi duba cancanta a wannan lokacin fiye da ɗan yanki ko ɗan ƙabila.

Wannan duk don amfanin ƙasar ce da tabbatar da cigaba da zaman ta dunƙulalliya. Dun wani abu da ‘yan siyasa za su yi matuƙar zai kawo tangarɗa ga haɗin kan ƙasa to a guje shi. In an tuna gwagwarmayar da a ka yi wajen kafa ƙasar da neman ’yanci to ya zama mai muhimmanci a kare ƙasar daga ƙara shiga halin rabuwar kawuna da burin kashin kai.

Idan shugabanci ne irin na siyasa ya na da wa’adi amma qasar ita kaɗai ce ta na nan kamar yadda a ke cewa bariki na nan amma soja zai zo ya tafi wani ma ya zo ya yi aiki. Zaɓen nan na watan gobe zai zama zakaran gwajin dafin ɗorewar Nijeriya ko a ce zaman lafiyar ƙasar.

Sassan ƙasar sun yi nisa ga muardin yanki ko ƙabilanci ta yadda ido ya rufe ba a ma ganin gaskiya sam. Ga kuma masu maganar addini ta ɓarauniyar hanyar amfana da madafun iko ba lalle don amfanin addinin na su ba. Tsarin mulkin Nijeriya ya ba da damar duk wanda ya cika ƙa’ida ya tsaya takara ba tare da duba daga wace ƙabila, yanki ko addini ya fito ba.

Masu cusa addini ta bayan fage na iya yin haka don ta nan ne za su iya shiga lamuran gwamnati. Za ka ga mutum ba ruwansa da addinin sa ta hanyar taimakon addinin wajen gina wajen ibada, makarantu ko taimakawa malamai, amma in siyasa ta zo ya ga wata kofa sai ya cusa addini a ciki ya kawo dalilai da za su iya tada ƙura har idan mutane ba su yi dogon tunani ba sai sun biye ma sa kuma a ƙarshe in buri ya cika ya manta da su don dama ba bisa manufa mai kyau ya shigar da batun addinin ba sai don cimma muradinsa na amfana da gwamnati.

Don haka idan mutum ya kawo addini sai a duba abun da ya yi wa addinin a baya kuma a duba shin ya na ma yin ibada kamar yadda addinin na sa ya shumfiɗa? Idan an samu akasin haka zai a ƙauracewa yaudararsa a bi hanya mai ɓullewa. Idan kuma a ka ga ya na da addinin kuma ya na taimakon addinin sai a saurare shi amma ba ta yadda hakan zai kawo husuma a ƙasa ba.

Nijeriya na da addinai mabambanta kuma duk ‘yan ƙasa bisa tsarin mulki na da ‘yancin yin addinin da su ka yi imani da shi. Wannan mai addinin ba zai kori wannan ba, wancan ma ba zai iya korar wannan ba, don haka sai a bi tsarin da za a zauna tare ba da cutar da juna ba.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar an gudanar da zaɓen 2023 mai adalci inda za a damƙa ragama ga wanda mutane su ka zava. Shugaban ya bayyana haka ne a sanarwar sabuwar shekarar miladiyya 2023 da a ka shiga a farkon makon nan. Wannan na nuna alamun sauyi daga wasu kalamai da tsohon shugaba Obasanjo ya taba yi a wajajen 2007 cewa zaɓe lamari ne na a mutu ko a yi rai.

A lokacin zaɓen an samu gagarumar matsala inda tsohon shugaban hukumar zaɓe Maurice Iwu ya sanar da sakamakon zaɓe alhali ba a ma gama tattara sakamakon ba. Wannan ya maida hannun aggogo baya na tunanin ƙuri’a ka iya canja gwamnati ko za ta iya amfani wajen samun zabar wanda mutane su ka kaɗawa ƙuri’a.

Sanarwar ta taɓo lamuran ƙasa da dama kuma shugaban na nuna shekarar ta 2023 na da muhimmanci gare shi da kuma sauran ‘yan Nijeriya saboda ƙoƙarin da za a yi na zaɓe da za a samu sake miƙa mulki ga wata sabuwar gwamnatin farar hula.

Alwashin shugaba Buhari har kullum shi ne zai damƙa gwamnatin hannun duk wanda ya lashe ko kuma a ce ga duk wanda ’yan Nijeriya su ka zaɓa. Don haka ba lalle said an APC ne zai iya lashe zaɓe ba.

Ga lamuran tsaro shugaban ya yabawa dakarun tsaro bisa himmar da su ke yi inda ya ce za a ƙara ba su kwarin gwiwar aiki don dawo da zaman lafiya mai ɗorewa.

Masanin kimiyyar siyasa na jami’ar Abuja Dr. Farouk BB Farouk ya ce yanda kamfen ke gudana na nuna za a iya samun wani sauyi da ba a tava samu a zaɓukan da a ka gudanar a baya ba.

Jami’a a Sashen Labaru ta Hukumar Zave, Zainab Aminu ta nanata cewa hukumar za ta yi amfani da na’urar tantancewa ta BVAS da za ta hana duk wani yunƙurin maguɗin.

Za a gudanar da babban zaɓen a ranar 25 ga watan gobe da kuma ranar 11 ga watan Maris na shekarar nan.

Kamfen na cigaba da gudana tun fara shi a sheakarar da ta gabata

Kammalawa;

’Yan Nijeriya ba baki ba ne ga harkar zaɓe kuma an samu nasarar dogon mulkin farar hula ba tare da katsalandan na soja ba. Abun da ya dace a nan kowane vangare ya gudanar da harkar kamfen da shiga zaɓe cikin lumana don rufe duk wata ƙofar da za ta iya kawar da dimokraɗiyyar.

Masu azancin zance na cewa sai ‘bango ya tsage ƙadangare kan samu wajen shiga’.