Dalilin tuɓe wa tsohon Wazirin Bauchi, Bello Kirfi rawani

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce tsige tsohon minista, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi da aka yi a matsayin Wazirin Bauchi hakan ba shi da nasaba da alaƙarsa da ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Gwamnatin Bauchi ta bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Hon AbdulRazak Nuhu Zaki, a wata hira da BBC Hausa ta yi da shi ranar Asabar.

A cewar Kwamishinan, sau da dama tsohon Wazirin ya janyo wa Masarautar Bauchi ɓacin suna, kuma bayan gargaɗin da aka yi masa Majalisar Masarautar ta ga dacewar ɗaukar matakin ladabtarwa a kansa.

“Ba gaskiya ba ne cewa da ake yi an tuɓe tsohon Wazirin ne saboda alaƙarsa da Atiku Abubakar ko kuma magoyin bayan ɗan takarar PDP ne.

“Sa’ilin da Atiku Abubakar ya zo Bauchi, bayan da ya gama jawabinsa, Gwamna ne ya kamata ya yi jawabi bayansa amma sai tsohon Wazirin ya buƙaci a ba abin magana.

“Duk da Gwamna ya buƙaci a miƙa masa abin magana, ganin haka tsohon Wazirin ya koma wurin zamansa tare da yi wa Gwamnan ƙananan maganganu.

“Kuma magana ta gaskiya, ba wannan ne karon farko da ake tsige tsohon Wazirin ba.

“Sarkin Bauchi, Dokta Rilwanu Suleiman Adamu ya dakatar da shi a 2017 saboda wasu kurakuransa, Mai Girma Gwamna Bala Muhammad ya roka aka maida shi shekaru biyu da suka gabata.

“Don haka tsige shi da aka yi ba ya da nasaba da siyasa ko goyon bayan Atiku Abubakar, abu ne da ya shafi sarauta da kuma neman kare sunan Masarauta,” in ji Kwamishinan.