Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato
Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato ta ƙaddamar shirinta na ƙarfafa mata iyayen marayu na kiyon kaji da aka fi sani da KAZBO wato kaza, zabo da mata ɗari da suka fito daga gundumomi daban-daban.
Da yake jawabi lokacin ƙaddamar da shirin, Shugaban Zartarwar Hukumar ta Zakka da Waƙafi Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato), ya ce manufar wannan shirin shine ƙarfafa uwayen marayu domin su iya dogaro da kansu ta hangar kiyon kajin.
Ya bayyana cewa hukumar tasa ta samu ƙwarin guiwar ƙaddamar da wannan bisa nasarorin da aka samu tun fara shirin shekara biyu da suka gabatar, inda wasu da suka amfana suka samu damar mallakar awaki da sauransu.
Akan haka ya buqaci matan da su ma su jajirce domin ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu ta hanyar bada kulawa ta musamman ga kajin.
Malam Muhammad Lawal Maidoki ya yi alƙawarin cewa duk waɗanda suka yi abin a zo a gani to hukumarsa za ta duba yuyuwar sake tallafa musu da jarin sana’a insha Allahu.
Daga nan ya ja kunnensu cewa kada su kuskura su sayar da kajin ko ƙwai don ba shi ne manufar shirin na KAZBO ba.
Babbar manufar a cewarsa ita ce kajin su samar da zabbi, daga zabbi sai akuya, sai tunkiya har daga ƙarshe a mallaki saniya.
Ya ƙara da cewa hukumarsa za ta cigaba da sanya ido domin tabbatar da nasarar shirin na ƙarfafa mata marar galihu a cikin al’umma musamman mazauna karkara.
Malam Muhammad Lawal Maidoki ya jinjina wa Ƙungiyar Mata Musulmi MSO wanda ta taka rawa ta musamman wurin samun nasarar KAZBO a Jihar Sakkwato bisa ga haɗin guiwar dake tsakaninsu wannan shirin.
Kowace daga cikin matan ɗari ta samu kaza huɗu da qwan zabo arba’in da kuɗin sayen kwandon kiwo. Ko kuma kuɗi Naira dubu tara da ɗoriya.
Shugaban hukumar ya jinjina wa kwamitin dake kula da shirin ƙarƙashin jagorancin Malam Umar Torankawa da Malama Amamatu Yahaya ta MSO.
Wasu da suka tava amfana, sun bayyana irin alfanun da suka samu.
Taro da aka yi a farfajiyar ofishin hukukumar ta zakka da waƙafi ya samu shaidar shugabar ƙungiyar Mata Musulmi ta Ƙasa Malama Amina Musa Sakaba, manya da ƙananan ma’aikatan hukumar da ‘yan jarida da sauran jama’a.
