Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Ɗaya daga cikin fitattun matasa masu tallafa wa jama’a kuma ɗan Jamiyyar NNPP Hon. Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Ɓoye ya bayyana cewa ɗaukar Fasto Isaac Idahosa, fitaccen mai wa’azi da rubuta waƙoƙi na Kirista, a matsayin mataimakinsa a takarar shugaban ƙasa a jam’iyya mai kayan marmari abin ya yi musu daɗi, kuma a cewarsa hakan ya nuna cewa jagora mutum ne mai hangen nesa, ƙoƙari da neman haɗin kan Nijeriya domin kawo zaman lafiya da ƙaruwar arziki idan ya zama shugaban Nijeriya a 2023.
Ogan Ɓoyi ya bayyana hakan ne a lokacin wani gaggarumin taro na tarihi da zumunci da ya kira a gidansa da ke Kano wanda ya samu halartar ɗimbin mutane daga sassa daban-daban na Nijeriya har ma da wajen ta wanda ya gudana a ranar Asabar da ta gabata.
Har ila yau ya ce, “ita tafiyar mu ta Kwankwasiyya tafiya ce ta fahimtar juna da yadda da jagora da miƙa masa wuya na amincewa na cewa ba zai ci amanar mabiyansa ba da sauran al’umma ba, don haka ba mu shiga tafiyar Kwankwaso ba sai da muka yarda jagora ne, don haka duk abin da ya yi ba ma ɗar! Mun ji, mun kuma bi.”
Haka kuma ya yaba wa ɗaukacin shugabannin sa manyan malamai da su ka yi jawabi na sanya albarka, irin su Khalifan Sheikh Aliyu Harazimi, Sarkin Malamai Alhaji Sabo, da Alhaji Rayyanu Muradun, Abdulmajid Agege, Alhaji Rabilu Okko, sai shugabannin kamfanoni kamar na Ta`ala, sai na Tababa, Alhaji Lawan Kaduna, da kuma shugabanni na siyasa irin su shugaban Jam’iyyar NNPP Hon. Haruna Doguwa, Hon Injiniya Abba Kabir Yusuf ɗan takarar Gwamnan Kano da mataimakinsa Hon. Abdulsalam Gwarzo, da Hon. Kawu Sumaila da sauran al’umma manya da ƙanana da suka halarci wannan taro mai ɗimbin tarihi ciki har da mutanen APC da sauran jam’iyyu wanda ya nuna cewa siyasa ba gaba ba ce.
