An ce yaro ka bar murna karenka ya kamo zaki. Na yi wannan rubutu ne domin faɗakarwa ga mutanenmu na Arewa a bisa lura da siyasar kudu. Jihar Osun an kammala zaɓe kuma Jam’iyyar PDP ta yi nasara ga gwamnati mai ci ta APC.
Da farko ina taya magoya bayan PDP murnar nasara tare da jajenta ma Jam’iyyar APC ta yadda gwamna mai ci ya zamo mai barin gado duka hakan ke fidda samun cigaba a siyasa.
Amma a arewma har yau da a kwai matsala? Zave ya gudana ba bu zage-zage kuma ba bu tozarta juna domin bambancin jam’iyya.
Kuma kwatamta zaɓen jihar Osun da zaɓen 2023 tamkar rashin kwakkwaran sanin siyasa a Arewa da kudanci ta ke. Da fatan a duk idan mun samu nasara ko akasi mu dunga magana a cikin hankali da nutsuwa. Allah ya kai mu zaɓen 2023 lafiya.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519/08080140820.
