Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
An bayyana cewa zaɓo mataimakin Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, a ba shi takara ta neman zama gwamnan Kano mai gadar Gwamna Ganduje, iya siyasa ne, gogewa da ƙwarewa irin ta Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Alhaji Auwal Ahmad Shinkafi, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar sansanin Alhazai ta Kano a lokacin da yake jawabi a sansanin Alhazan a ranar Litinin da ta gabata.
Shinkafi ya ce Gwamna Ganduje da mataimakinsa kuma ɗan takara Gwamnan Kano a 2023 sun taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkar kasuwanci a Kano, ta hanyar gina-gine a kasuwar Kantin Kwari da sauran kasuwanni irin su Hajji Camp, wanda a cewarsa su ma shaida ne na wannan cigaba na gine-gine wanda cigaban ne da suka samu da taimakon Ganduje da Gawuna wanda ya kawo wannan cigaban kasuwar ɗari bisa ɗari wanda hakan ce ta sa ‘yan kasuwar kashi 90 cikin 100 APC suke yi, a cewar Alhaji Auwal Ahmad Shinkafi.
Ya ƙara da cewa Dakta Nasiru Gawuna shi ne xan takarar Gwamnan Kano da ke da kyakyawar mu’amala da girmama manyan ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, malamai, sarakuna, da sauran al’ummar Kano, kuma shi ne abin da Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya lura da su ya bai wa Gawuna takara.
Shi ma Alhaji Aminu Bako Gama, jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar kasuwar Hajji Camp, a. Asa jawabin, cewa ya yi shekaru sama da biyu da shugabancin shugabansu Alhaji Auwal Ahmad Shinkafi kasuwa ta samu cigaban da ba a taɓa samu ba a tarihi, kasuwar kuma ya zama mai taimakon musamman a matsalolin da aka samu na rashin ciniki sakamakon tashin farashin kayayyaki da matsalar rashin zuwa aikin Makka, da ba a yi ba a 2019 da 2020 saboda annobar Korona, kuma har yanzu ya na taimakawa ga raunana da mara sa lafiya a wannan kasuwa da yawaita addu’ar Allah ya bada zaman lafiya a Kano da Nijeriya baki ɗaya.
