Za mu gina Nijeriya kamar yadda muka gina Lagos da Borno – Shettima

Spread the love

Daga IBRAHEEM HAMZA MUHAMMAD

Sanata Kashim Shettima ya jaddada cewa, Najeriya za ta mori romon mulkin dimukraɗiyya idan aka zavi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin Shugaban Ƙasa a zaven da ke gabatowa.

A takardar sanarwa da Kakakin Kwamitin APC mai neman a zaɓi Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima a matsayin Shugaba da Mataimaki, Mista Bayo Onanuga, ya fitar, ta ce, sanatan ya furta haka ne a ranar Litinin a Legas yayin da ya wakilci Tinubu a taron shekara-shekara na Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA). Inda ya ce, aikin gani-da-ido da Tinubu da Shettima suka aiwatar a Lagos da Borno ya zama manuniyar cewa su masu aiki tuƙuru ne.

Tsohon Gwamnan na Borno ya ce, duk da yanayin rashin tsaro a Arewa Maso Yamma yayin da yake mulki, ya taka rawar gani a fannin ilmi.

Sanata Shettima ya ƙara da cewa, “jama’a suna da alhakin su yaba wa mai aiki a maimakon mai yawan dogon Turanci.

“Ya dace jama’a su bi wanda ya san hanyar zuwa ga ɗaukaka, domin in an zaɓe mu, a ranar farko za mu fara aikin yalwata tattalin arzikin ƙasa, samar da yanayi mai alfanu da kuma inganta tsaro.

“Da Tinubu da ni gwaraza ne da muke son gina ƙasa: Alal misali, ana iya zuwa Jihar Borno, don gani-da-ido kan yadda na gina makarantu, sannan kuma na inganta samar da ilmi gadan-gadan duk da ana yaki da masu ɗauke da makamai a lokacin.

“Ba za mu yi ƙasa a gwuiwa ba wajen kambana ayyukan da muka yi a jihohinmu, don ciyar da jama’a su sami bunƙasa.”

“A taƙaicen-taƙaitawa, mun ƙuduri aniyar yin jagoranci na gari,” a cewar Sanata Kashim Shettima.

By Editor