Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Na san wannan take na yau zai tayar da hankalin wasun mu da dama, musamman malamai, alarammomi da ɗaliban ilimi, da ma uwa uba iyaye. Ba na zaɓi in yi wannan faɗakarwa kan almajirai ne kaɗai ba, har ma da sauran yaran mu da ke rayuwa a gaban iyayensu.
Na san ba ni kaɗai ne wannan al’amari ke damuna ba, lura da yadda ake cigaba da samun taɓarɓarewar tarbiyyar yara ƙanana da ke samun kansu a cikin wata irin gurɓatacciyar rayuwa marar tsafta, saboda rashin kulawar iyaye, sa ido daga manya masu kula da tarbiyya, har ma da malamai da ake bai wa amanar kula da ba su kyakkyawar tarbiyya da ilimantarwa.
Ba na mantawa, a unguwar da na taso akwai wata babbar makarantar tsangaya inda daruruwan yara almajirai daga sassa daban-daban na Arewacin ƙasar nan ke zuwa da malamansu da wakilan su don neman ilimin Alkur’ani, don zama a gaban babban malamin da ya kafa wannan makaranta.
Sai dai abin damuwa da takaicin shi ne, yawan yaran ya sa ba kowanne yaro ne malaman ke iya sa ido a kansa ba, wasu tun rana in sun tashi a makaranta ba a sake ganin fuskokin su, sun fita barar neman abinci, ko karatun yamma da ƙyar suke dawowa. Wasu kuwa idan sun dawo na yamma to, su da dawowa sai kusan sha biyun dare, sun tafi bara bakin tasha ko bakin sinima da gidajen karuwai.
Akwai wasu daga cikin yaran da na kiyaye da su, waɗanda sau da dama nake haɗuwa da su a hanya suna fita ko dawowa, ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, na sha kora su makaranta ko in yi musu faɗan kai wa dare a inda suka je, ko kuma nuna fushina kan irin wuraren da suke zuwa.
Ina iya tunawa da har wasu abokaina daga malaman su na sha kai wa kukan abubuwan da yaran ke yi, don a tsawatar musu kuma a ɗauki matakin da ya kamata tun da wuri.
A lokacin da muke tasowa, muna yara a makarantar allo akwai wani daga cikin matasan gardawan da suke koyar da mu a lokacin ana ce masa Walagigi, saboda da ƙin jin sa, amma duk da zafi da hukuncin da malamin mu na makaranta, da ake yi wa laƙabi da Hukuma, ya ke yi masa bai hana almajirin nan lalacewa ba, daga bin gidajen karuwai sai zuwa bin dabar da aka san ɓarayi ne ke sabga a wajen.
Ganin haka ya sa Malamin mu ɗaukarsa ya mayar gida wani yanki da ke tsohuwar Jihar Sakkwato, amma bayan wani lokaci sai aka sake ganin Walagigi ya dawo ya cigaba da harkokin sa a gari, ba tare ma da waiwayar makaranta ba.
Waɗannan kaɗan ne daga cikin misalan da zan iya bai wa mai karatu na dalilan da suka sa ni wannan tunani tun a baya, da kuma abubuwan da a yanzu haka suke faruwa na taɓarɓarewar tarbiyyar yara almajirai a birane da ƙauyuka, wanda ana iya samu daga halayyar yaran da ke rayuwa a gaban iyayen su, kamar yadda na yi nuni da shi a baya.
Sai dai inda ake samun bambanci shi ne su yaran da ke gidajen iyayen su suna da iyakar abin da za su iya yi, saboda yawan sa ido da tsawatarwa da suke samu a gida, kuma idan an yi sa’a da iyaye masu kula sosai, da zarar yaro ya fara wasu baƙin halaye nan da nan za a taka masa burki.
Amma bambancin matsalar a wajen almajirai da ke karatu nesa da iyaye kuma ba sa samun kusanci da malamansu na tsangaya sosai, shi ne idan sun fita titi ko bara rayuwarsu na gamuwa da ƙalubale iri iri, lalacewar wasu manya da fitsararrun yara da ke gudun iyayensu da abubuwa na savo da ke faruwa a kan idanun su yana kangarar musu da zuciya ko ya ja hankalinsu, kamar dai yadda ta faru da Walagigi a cikin misalin da na kawo na baya.
A nan ba ina cewa dukka yaran almajirai lalatattu ba ne ko kuma dukkan yaran da ke gararamba a titi suna tambaɗa yaran da ke gujewa daga makarantun allo ba ne, amma dai tunatarwar da nake so in yi a wannan gaɓar kan almajiran makarantun tsangaya ne.
Babu shakka akwai abin tashin hankali da damuwa ka ga yaro ƙarami wanda ake sa mai rai da zama malami, kuma jagora nan gaba idan Allah ya ja kwana, a ga ya taso yana wasu halaye da ba su kamata ba, ko kuma yana shiga inda ke da haɗari ga tarbiyyarsa da rayuwarsa.
Kuma na san babu wani malami ko uba da zai ji daɗin ganin ɗan sa ko ɗalibin sa yana aikata wani abu da al’umma za ta yi tir da shi. Sai dai wani lokaci babu yadda mutum zai iya, don kuwa ko da kana yin naka ƙoƙarin a gida ko a makaranta, abokai, ko al’umma da muhallin da yaro ke rayuwa a ciki, suna da gudunmawar da suke bayarwa wajen warware abin da ka ke ƙullawa na alheri a rayuwarsa.
Wani abin takaici da ya ke faruwa a yanzu shi ne na yadda wayoyin hannu masu ƙirar android suka yi yawa a hannun yara, saɓanin a shekarun baya. Yayin da wasu iyayen ke saya wa yaransu da kansu don su riƙa tuntuɓarsu a duk inda suke, wasu kuma suna saya musu ne don ya taimaka musu wajen aikin makaranta, ko kuma don gata, da burgewa.
Sai dai a yayin da aka bai wa yara masu ƙananan shekaru waya ko waɗanda suke cikin shekarun balaga, mai ake tunanin za su iya yi da waɗannan manyan wayoyi?
Wani bincike da aka gudanar ya bayyana cewa, yaya qanana da suka damar kallon bidiyon batsa da wasu finafinai da ba su kamata ba, suna iya tasowa da wasu halaye da za su iya cutar da rayuwarsu da alaƙarsu da sauran jama’a, musamman alaƙar mace da namiji.
Yara maza za su iya tashi da jarabar son mata, ko halayyar kin daraja ’ya mace da wulaƙanta ta ko cin zarafinta da yi mata fyaɗe. Haka ma a vangaren mace za ta iya tashi da rashin sakewa da mutane, tsoron namiji ko kai kanta ga inda za a wulaƙanta rayuwarta da mutuncin ta na ’ya mace, don tana ganin hakan shi ne soyayya.
Ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, wasu iyaye masu tsauri da sa ido da yayye masu wayewa kan harkokin rayuwa sun sha bayyana yadda suke ganin wayoyin yaransu ko ƙannensu cike da bidiyo da hotuna marasa kyan gani, da ke nuna tsiraici da yadda mace da namiji ke saduwa tsirara, da sauran abubuwa na batsa. Wa’iyazubillah!!!
Wani ya taɓa ba da labarin yadda wata ƙanwarsa ke shiga manhajar Google ko YouTube a babbar wayar da aka saya mata don aikin makaranta a ɓoye, don kallon bidiyon batsa, da tunanin ba za a gane ba, amma saboda yana da ilimin gano waɗannan sirruka, ba tare da ɓata lokaci ba ya gano abin da take yi, har kuma ya ja hankalin iyayensu kan abin da ke faruwa.
Wasu yaran a makarantar ne ma suke haɗuwa da abokai ko ƙawayen da suke tura musu irin waɗannan munanan hotunan batsa da bidiyo suna ɓoyewa a waya suna kallo.
Waɗannan ga yaran da ke gaban iyayensu a gida kenan kuma suke samun gatan karatu, to yaya kuma ga wasu yaran da ba su kai waɗannan shekarun ba ko kuma ba su ma samu gatan shiga makarantar boko ba, kamar almajiran da na yi magana a baya? Ko ba ka taɓa ganin yaran almajiran da aka kama wayoyinsu da irin waɗannan hotuna da bidiyon batsa ba?
A yayin nake haɗa wannan rubutu a wata anguwa cikin birnin Kano, wasu mutane sun lura da gungun wasu yara almajirai sun zagaye wani yaro a tsakiyarsu suna kallon wani abu a waya suna dariya, dubawar da suka yi kuwa sai ga shi suna kallon wani bidiyo ne na batsa, da ke nuna wasu mace da namiji suna lalata da juna.
Wata ’yar jarida kuma mai nazari kan rayuwar mata da ƙananan yara, Rabi’atu Sidi Bala, ta koka kan yadda wannan abu ke neman zama ruwan dare a tsakanin yara matasa, musamman almajirai da mutane ke kuka da yadda suke aikata wasu abubuwa na rashin tarbiyya da ba su dace da ɗaliban Alqur’ani ba. Wasu abubuwan da suka haɗa da shaye-shaye da sata, da sauran halayen assha.
Shugaban Ƙungiyar Inganta Karatun Tsangaya ta ƙasa, Gwani Jibrin Yahaya Alƙasim ya bayyana baƙin cikinsa da wannan mummunan al’amari da ke faruwa a rayuwar wasu yara almajirai, inda ya yi kira ga malaman makarantun allo su ƙara tashi tsaye don ganin sun kula da abubuwan da yaran da aka ba su amanar ilimantar da su suke yi, tare da ɗaukar dabarun tarbiyya da tsarin gudanarwa na zamani, saboda yadda yanzu rayuwa ta canja.
Sai dai ya bayyana cewa, irin wannan al’amari na taɓarɓarewar tarbiyya ba a kan almajirai kaɗai ya tsaya ba, wani lokaci ma daga ɗaliban makarantun boko irin wannan baɗala ke fitowa.
Ya nemi iyaye da sauran al’umma masu kishin tarbiyya su taimaka wajen tsawatarwa da kai kukan irin waɗannan yara almajirai ga malamansu ko makarantun su, don ɗaukar matakin da ya dace.
Wannan shawara ta zo daidai da nasihar da Dr Gwani Danjuma Usman na Tsangayar Nazarin Harshen Larabci a Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe ya yi, inda shi ma ya bayyana takaicinsa game da irin wannan mummunar halayya da ake samu daga wajen yara almajirai, yayin da ya buƙaci malamai da iyayen yara su dage da ba da tarbiyya ga yaran da Allah ya ba su amanar kula da kiwon su.
Ya kuma ɗora alhakin wannan abu da ke faruwa kan lalacewar zamani da ya kawo wannan gurɓacewar tarbiyya, sakamakon bazuwar waya a hannun mutane, wanda ya ce ba ga yara ko almajirai kaɗai wannan al’amari ya shafa ba, har da sauran jama’a. Kowa na da alhakin kiyaye abin da yake aikatawa da wayarsa, don ya kiyaye mutuncinsa da lahirarsa.
Sannan ya kamata mutanen anguwa su ma su ba da irin ta su gudunmawar wajen sa ido kan shagunan masu tura waƙoƙi da finafinai a waya, saboda yawanci a wajen su ake samun irin waɗannan bidiyo da hotuna na batsa da ake tura wa yara ƙanana a wayoyin su. Da shagunan sayar da magunguna na cikin anguwa da ake sayar wa yara ƙwayoyi masu bugarwa!
Ya kamata iyaye su ji tsoron Allah, su kula da makomar rayuwar ’ya’yansu, in har bai zama dole ba, su daina barin manyan wayoyin da za a iya tura hotuna ko bidiyo a hannun yaransu, in dai ba wanda za a amsa kira ba, in ma saboda yin aikin makaranta ne, a bari idan sun dawo gida sai su yi amfani da wayar maman su ko babansu ko wani yayansu da ke gida. A daina bari suna fakewa da saka manhajojin wasanni na ɗebe kewa ne ko sa karatun Alƙur’ani a ciki.
Sannan in ta kama tilas a bar su da babbar waya, akwai wasu hanyoyi da iyaye za su kulle duk wani shafi mai tura bidiyo ko hotunan batsa ta yanar gizo daga wayoyin yaransu, don kada shiga wayoyinsu nemo irin waɗannan shafukan batsa suna kallo.
Lallai ne malaman makarantun boko da na allo su ƙara tsaurara matakan hana yara zuwa makaranta da manyan wayoyi da ƙwace duk wata waya da aka gano ana yin abin da bai kamata ba.
Shugaban Ƙungiyar Malaman Tsangaya, Gwani Jibrin Yahaya ya yi kira ga malaman makarantun allo su ba da haɗin kai a ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi na tsaftace harkar karatun allo, da shigo da tsare-tsaren zamani da za su kawar da ƙyama da tsangwamar da ya ce ana nunawa almajirai da makarantun tsangaya.
