Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Duk wanda ya fito a farkon makon nan a cikin babban birnin Nijeriya, Abuja zai ga mutane su na hada-hadarsu tamkar ba wata barazanar yiwuwar kawo hare-haren ’yan ta’adda. Haƙiƙa sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka da ke nuna akwai barazanar kawo harin ta’addanci musamman a Abuja ya zama abun zantawa da yaɗawa a kafafen labaru amma a gefe guda kai tsaye hakan bai sauya yadda talakawa ke shiga kasuwanni ko gidajen da sauran su don harkokin yau da kullum ba.
Ai wasu ma dama sun dawo Abuja ne don garuruwansu sun yi zafi a na ta kashe-kashe da sace mutane. Don haka gargaɗin yiwuwar kawo hari ba zai firgita wasu su riqa takatsantsan ba. Kazalika dama birnin ya faye yawan ƙananan ma’aikata waɗanda kan shigo da safe su yi aiki da yamma kuma su bazama su nufi kauyukan su ko unguwannin su na bayan gari.
Duk da haka in an duba gargaɗin ofishin jakadancin na magana ne kan Amurkawa da ke birnin don su yi kaffa-kaffa da yadda su ke hulɗar su a birnin. Ba mamaki duk Amurkawa sun dau wannan gargaɗi da muhimmancin gaske don ba za su zama masu wasa da bayanan sirri ba don kare kan su. Burtaniya ma ba a bar ta a baya ba wajen fidda irin wannan gargaɗi ga ’yan ƙasar ta cewa akwai barazanar ’yan ta’adda na kitsa kawo hare-hare Abuja.
Irin wannan gargaɗi na daga ayyukan ofisoshin jakadanci ga ’yan ƙasa da ke ketare don kula da lafiya su da dukiyarsu. Akwai kalolin nan na Hausawa da ke cewa yaron da ba shi da uba wato maraya ya saurari gargaɗin mahaifin abokin sa ko wani na sa kan lamuran rayuwa sai ya dau darasi a ciki.
Dole ne gargaɗin ya yi tasiri ga ’yan boko da hamshaƙan masu hannu da shuni waɗanda ko ciwon kai ne ya same su sai sun ruga ƙetare don ganin likita. Ma’aikata talakawa na fama da ƙarancin albashi da jibgin matsalolin rayuwa don haka zai yi wuya a lokaci ɗaya su iya kaucewa taron jama’a don wannan gargaɗi.
Tun gabanin gargaɗin dama birnin kan tara motoci a gidajen mai don neman man fetur da ya yi ƙaranci ainun bida dalilan motocin dakon fetur din ba sa samun isowa cikin sauƙi don ambaliyar ruwa a hanyar da su ke bi don shigowa Abuja. Wasu direbobin ma musamman na tasi kan kwantar da kujera su kwana a cikin mota don bin layin mai.
Ba a ga gagarumin sauyin wajajen binciken motoci ba a sanadiyyar wannan gargaɗi don dama ba daga hukumomin Nijeriya ya fito ba. Wani abun dubawa shi ne yadda wasu da su ka ƙware da sanin kan garin kan bi wasu hanyoyi da su kan kaucewa wajajen binciken motocin na ’yan sanda kuma ba lalle don ba su da gaskiya ba ne a’a wasu daga cikin su don uzurin da ke gaban su ne da gujewa ɓata lokaci a wajajen binciken.
Wasu ma bas a son a tsayar da su don ba su da ra’ayin ba da na goro ga wasu jami’ai da kan so samun sulallan na Bello Badun. Babu dai tsarin yadda a ka yi Abuja akwai muhimman hanyoyi uku da matuƙar a ka datse su zai yi wuya mutum ya iya fita daga birnin zuwa Jihar Nasarawa ta kudu maso gabar, Kaduna ko Neja ta Arewa maso Yamma sai kuma babbar hanyar da ta nufi filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe inda mafita ce zuwa Gwagwalada kan hanyar Kogi har Legas.
A shekarun baya birnin ya yi fama da hare-haren boma-bomai da su ka yi sanadiyyar asarar rayuka. Wajajen da hare-haren su ka shafa sun hada da helkwatar ’yan sanda wato gidan Louis Edet, ofishin Majalisar Ɗinkin duniya, ofishin gidan jaridar Thisday, kasuwar Emab da ke anguwar Wuse 2 da sauran su. A cikin hare-haren har da na ƙunar baƙin wake.
A lokacin mutane kan shiga firgici matuƙar suka tsinci kan su a waje mai cunkoson jama’a. Tun wancan loakci bayan fara hare-haren boko haram a 2009, jami’an tsaro su ka raba titunan gaban ofisoshin su don ƙange hari.
Har yanzu waɗannan shingaye na nan a gaban ofishin ’yan sanad, ’yan sandan farin kaya, helkwatar sojoji da wasu ofisoshin jami’an da ke birnin. Gargaɗin na zuwa ne a lokacin da hankali ke kwance kuma mutane ke ɗaukar kan su a tudun mun tsira matuƙar su ka shigo Abuja.
Gaskiya za a iya cewa tudun mun tsira don a nan a ke da fadar Aso Rock, majalisar dokokin taraiya da kotun koli. Ga barikokin soja barjak da na’urori da ke ganin abubuwan da ke gudana a birnin. Idan kuwa Abuja ta sake komawa waje mai ban tsoro to lamarin ya kai ɓacin da sai gyaran Allah kawai don kuwa ai iya waje mai tsaro kenan.
Duk manyan ƙasa na da masauki ko ma gida a Abuja inda su kan zo su zauna don sararawa bayan shiga garuruwan su ziyara ko kamfen ɗin siyasa. Anguwar Asokoro da Maitama a matsayin manyan unguwannin alfarma na cike da irin waɗannan mutane da ke samun kariyar ’yan sanda.
Idan an ga raguwar zirga-zirgar irin ajin waɗannan mutane bayan fitowar wannan gargaɗi ba za a yi mamaki ba don dama a na zaune kalau ma kullum da rundunar ’yan sanda su ke yawo. Lamuran tsaro sun shafi kowa ne ta yadda ya zama mai muhimmanci mutane su riqa sanin duk waɗanda su ke mu’amala da su da sauye-sauye da ka iya ɗaukar hankali har ya kawo kokonto.
Akwai wajajen ma mutum ya san zuwan sa ko ba gargaɗi ka iya kawo barazana ga rayuwa. Wajajen sun haɗa da kulob-kulob inda ’yan duniya hayaqin taba kan sheƙe aya da gidajen shan giya. Wasu wajajen sun haɗa da ƙarƙashin gadoji inda ba mutane kusa da wasu unguwanni da ke da dazuka ko lambuna masu duhu.
In da mota mutum ya ke tafiya ya na da kyau ya san inda ya dace ya tsaya sannan ko bayan ya tsaya ya ƙaranci wajen tukun kafin buɗe motarsa. Hanyoyin kare kai a fili su ke.
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa ta na bitar ankararwar da ofishin jakadancin Amurka ya yi da ke nuna akwai barazanar kawo hare-haren ta’addanci a Nijeriya musamman kan Abuja.
A sanarwa daga kakakin rundunar Olumuyiwa Adejobi, rundunar ta ce a matsayin ta na kan gaba a lamuran tsaron cikin gida ba za ta yi sako-sako ga duk wata barazana ba don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar jama’a.
Babbban sufeton ’yan sandan Usman Baba Alƙali ya umurci kwamishinan ’yan sanda na Abuja da sauran zaratan ’yan sanda a birnin su ƙara ɗaukar matakan tsaro. Bayan nan ya umurci sauran kwamishinonin jihohi ma su ɗauki matakan kula da tsaron jama’a.
Hakanan rundunar za ta gudanar da wani atisaye a harabar helkwatar ta da ke Abuja da kuma makaranta mallakar matan ’yan sandan da ke ɗaura da helkwatar don kaifafa dabarun yaƙi da ta’addanci.
Rundunar ta ce a lokacin atisayen mai taken ‘DARKIN GAGGAWA’ kamar yadda sanarwar ta ambata za a karkatar da akalar motoci zuwa wata hanya don gudanar da shirin a tsanake.
Ita ma rundunar tsaron farin kaya ta Nijeriya DSS ta baiyana cewa gargaɗin da Amurka ta yi na bazaranar kawo harin ta’addanci ba sabon abu ba ne wato ma’ana an saba samun irin hakan a baya.
A sanarwa daga kakakin rundunar Peter Afunanya, DSS ta ce in za a tuna ita kan ta, ta sha fitar da irin wannan gargaɗi a baya don ankarar da jama’a shirin kawo hari.
DSS ta ƙara da cewa za ta yi aiki da sauran hukumomin tsaro don daƙile bazaranar don haka kar mutane su firgita bisa ma’ana su cigaba da harkokin su na yau da kullum.
Rundunar ta DSS ta kara da cewa ya na da kyau mutane su riqa takatsantsan da kuma taimakawa jami’an tsaro da duk bayanan da za su ƙara taimakawa wajen kawar da barazana.
DSS ta ce ta samu tambayoyin buƙatar sanin halin da a ke ciki tun fitar da sanarwar ta ofishin jakadancin Amurka; da hakan ya sa ya zama mai muhimmanci ta fito da wannan bayani.
Kammalawa;
A wannan zamanin tsaron rayuka da dukiyar jama’a ya zama abun tattaunawa da kula a kullum don yadda a ka samu taɓarɓarewar tsaron. Kuma abun dubawa rashin tsaron ba da salon yaƙi ne tsakanin ƙasa da ƙasa ko wata runduna da ta ke gefe ɗaya da muradi ɗaya ba, irin wannan yanayi ya shafi wasu miyagun iri ne da kan fake a cikin jama’a kuma ba ma lalle su na da wata kala ko shaidar da za a iya gane su ba.
Wani abun dubawa miyagun kuma ba dukan su ne ma za a ce daga wata ƙasa su ke zuwa ba, an tabbatar da yawa daga cikin su ’yan Nijeriya ne. Wasu ma da a na tare da su amma wasu dalilai su ka saka su ka bijire.
Wasu bayanan kuma na nuna akwai masu ɗaukar nauyin miyagun da a kan samu a cikin jama’a. Ya na da kyau in an kashe maciji a sare kansa amma amfani da dabarar a ciza a hura na sunnar ɓera na da amfani.
