Tare da BASHIR MUDI YAKASAI
Babban labari a duk kafofin labarai na duniya a wannan makon shine duniya ta amince da ta daina amfani da duk wani makamashi da ke da haɗari wajan kawo ɗumamar yanayi, inda aka lissafa man fetur da gas da sauran dangogin su tare kwal. Amma abin mamaki ƙasashe sama da ɗari biyu (200) su suka sanya hannu bayan jefa ƙuri’ar amincewa.
Taron ɗaya gudana a ƙasar haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a birnin Dubai ya zo da bazata domin kuwa an kwashe sama da shekaru 30 majalisar ɗinkin duniya tana fafutukar jawo hankalin duniya haɗarin da yake tattare da sauyin yanayi inda masana suke ta hangowa duniya illar da take tattare da shi sauyin, amma ita majalisar ta duniya ta zama ’yar amshin shata, saboda ga jaki amma ake dukan taiki.
Su na manatawa cewa aƙidar tara abin duniya wacce ƙasar Amurka take jagoranta da sunan damakuraɗiyya tun bayan yakin cacar baki da aka gwabza tsakanin ta da (Union of Soviet Socialist Republic (USSR)), wacce ƙasar Rasha ta yanzu take jagoranta. Wannan aƙida da Amurka wato USA da ‘yan kanzaginta ƙasashen yammacin turai, United Kingdom, Faransa, Jamus, Fotugal da sauran mambobin ƙungiyar su ta tarayyar turai (EU) da suke kururuwar sheɗan GDP na gas.
Kowacce ƙasa ta tashi haiƙan wajan binciko makamashin (crude oil), inda duniya kan sha sama da ganga 100 a kullum ta Allah, inda wasu ƙasashe suke facaka sa kece raini da kuɗaɗen makamashin man fetur da gas, wasu ma hadda kwal. Inda waɗannan ƙasashe suke ci da gumin wasu domin sune suke bincike inda man nan da gas da suke kwance a ƙarƙashin ƙasa da ƙarƙashin tekuna miliyoyin shekaru sun sanya guguna suna ta kwasa suna kaiwa ƙasashen su domin biyan buƙatunsu na yau da kullum su bar ƙasashen da wannan makamashi na man fetur yake cikin faɗace-faɗace a tsakanin ‘yan ƙasar da tarzoma launi-launi baya ga fatara da talauci da yunwa da cututtuka marasa kan gado uwa-uba baƙin jahilci da duhun kai.
Shawara ta farko ita ce: yaya za wayar da ‘yan ƙasa cewa nan da shekara ta 2030, wato shekaru shida ga mai yawan rai kasuwar man fetur za ta sake salo, don haka ƙasashe masu taƙama da hura hanci, domin kuwa da shi ’yan ƙasa kuma ‘yan ƙasar ƙalilan sune suke cin moriyar makamashin da ake fita da shi zuwa yammacin inda suka gina hanyoyi da mugudanan ruwa da asibitoci da ɗakunan shan maganin wata ta zo da sauya tafiya a faggen ilimi a koma “functional education” ga matasan mu da gama makaranta sai aikin yi.
Wata shawara ita ce wayar da kai: A wayar da kan ’yan Nijeriya sama da kashi 60 na ’yan ƙasa ba su san lokacin da tattalin arzikin wannan ƙasa shine noma da kiwo ‘yan Nijeriya su suke ciyar da masana’antun Ingila da Auduga da Gyaɗa da Rini da Kwakwar Manja da Kwara domin man Kaɗanya da Koko da ƙaro da ɗorawa idan muka ci gaba da lissafawa sai wasu ma su ɗauka zance kawai kurum muke yi. Baya ga kayan amfanin gona sai dabbobi shanu da tumaki da awaki da jakuna da Aladai banda tsintsaye kamar zabi da kaji da agwagi.
Daga 1908 zuwa 1960, a lokacin Nijeriya ta ɗauki kambun ƙasa a Afirka wajen tallata wa yammacin Turai gina ƙasashensu sama da kasha 45 na gine-gine da gidaje da hanyoyin mota dana jiragen ƙasa da dukiyar Nijeriya aka samar da su. Wannan ya sa suka bamu ladan gabe ta gina hanyar Legas, wato Ikko zuwa Kano zuwa Sokoto haka daga Fatakwal zuwa Jos zuwa Enugu Zuwa Maiduguri.
Baya ga haka suka gina hanyar Jirgin ƙasa daga Legas har zuwa ƙauran namoda da kuma wanda ya tashi daga Kano zuwa Nguru a Jihar Yobe ta yanzu. An yi haka ne domin a kwashi dukiyar amfanin gona da fatu da kuma ƙirgi zuwa tashoshin ruwa da suke Ikko da Fatakwal.
Babu mahalukin da zai iya ba ka lissafin al’ummar da ta halaka saboda wannan ayyuka na kwasar dukiyar amfanin gona da ma’adanai sun fi 50, kuma babu ɗan Nijeriya da zai shaida maka irin miliyoyin Ton na ma’adanai da suka kwashe zuwa yammacin Turai, wani abin baqin ciki ’yan Nijeriya haka suka yi wannan aiki a maho babu ko sisin kwabo shi da bauta babu maraba. Sai mu cigaba da addu’a da Allah ya qara nauyin ƙasa ga jagororin mulkin mallaka irin su Sir. Fredrick Lord Laggard.
Da mabiyansa Sir. Hugh Clifforf, Sir. Creamer Thompson, Sir. Author Richard, Sir. John Mcpheson da kuma Sir. James Robertson wanda a lokacin sa ne aka ba mu ’yan cin jeka-nayika, wato ’yan cin ɗaurin talala banda takunkumi da kuma dabaibayi. Allah ya jikan mutane irin su Sir. Abubakar Tafawa Balewa, Sir. Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto), Malam Aminu Kano, Dokta Nnamdi Azikiwe, Herbert Macauley da kuma Chief Obafemi Awolowo da sauran ’yan gwagwarmaya maza da mata.
Tun da taron Dubai ya nuna kuma ya haska ina aka dosa inda aka fake da sauyin yanayi zuwa aifishiyal intalijent. A harkar makamashi kuwa za a koma lantarki, hasken rana da kuma kaɗawar iska wanda Nijeriya tana da su jamfa a Jos. Saura da me hankulanmu su dawo jikin mu mu karkato zuwa ga ma’adanai kamar azurfa da tagulla da tama da kuza da tantalaite da zinariya da dai sauransu sun doshi 100. Kuma tun kafin zuwan turawa ake sarrafa waɗannan ma’adanai ta hanyoyi daban-daban kamar narkawa d bugawa da zubi da yin hatimi da yin rabiti.
Kamar yadda muke faɗa a kullum sarrafa ma’adanai a wannan ƙasa ba sabon abu ba ne, domin kuwa shi ya gina birnin Kano lokacin da Gayawa suka zo kwasar tama a Dutsen Dala da Gwauron Dutse da Panisau kuma sun gudananr da bincike (exploration) na waɗannan ma’adanai tun 999-AD a Rano da Tanagar da Ruruwai da Dawakin Tofa da kuma Dawakin Kudu duk a Jihar Kano ta yanzu. Duk wani birni da ka je a Arewacin Nijeriya za ka ga rawar da maƙera da kuma (Geologist), wato masana ilimin sanin ma’adanai.
Ƙalubalan da ke gaban gwamnatin Asuwaji Bola Ahmed Tunubu shi ne yaya zai ɗora Nijeriya akan wannan tafarki na Nijeriya babu cinikin man fetur kamar yadda tsohon daraktan zartarwa na kamfanin NNPC Mista Alex Ogedengbe durƙushewar matatun man fetur na Warri da Kaduna da kuma Fatakwal an gina su ne d tsohuwar fasaha ta tace ɗanyan man fetur ɗin, wanda ko an gyara ba za su gamsar da ’yan Nijeriya ba, ya kamata a hakura da su, wannan muna goyon baya domin kada a ci gaba da daven kwalo.
Ya zama wajibi a wannan shekara ta 2024 shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmaed Tinubu yayi garanbawul a hakumar NNPC da ma’aikatar ma’adanai a yi sabon zubi saboda ƙorafe-ƙorafe da suka yi yawa na badaƙala ta dukiyar ƙasa. Kuma a yi bincike mai zurfi kan manyan ƙasa kamar yadda ministan ma’adai ya baiyana cewa suna da hannu dumu-dumu wajan ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda awannan ƙasa.
Kamata ya yi ’yan sanda da DSS da EFCC da suka ji wannan maganar daga bakin minista su yi hanzari wajen bincike na gano mutanen da suke da hannu wajen wannan ta’asa, mu na da tabbaci idan aka ƙyale abin ya gwurta sai ya fi abubuwan da suke faruwa a yankin Niger Delta ko Boko Haram a yankin Borno da kuma ‘yan fashin daji na Kudancin Kaduna da sassan Zamfara da Kebbida kuma Sokoto.
Baya ga haka sai ma’aikatun tarayya da Jihohi da kuma ƙananan hukumomi 774 sun tsaya tsayin daka wajen yaya Nijeriya zata kasance ta daina dogara kacokan kan fetur, inda za ta koma kan noma da ma’adanai. Kuma kauce wa kuraren da Shugaba Shagari ya yi da shirinsa (Green Revolution) da shirin Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida nomansa na alkama da kuskuren da Shugaba Olusegun Aremu Obasanjo shi ma ya yi a noman Rogo da ya yi, haka da kuskuren shugaba Muhammadu Buhari na APC ya yi a nomansa na shinkafa.
Asuwaju Bola Ahmed Tunubu ga dama ta samu kai zaka gyara kurakuren da Janar Yakubu Gowon (1966 zuwa 1975) ya sauke Nijeriya daga noma da kiwo zuwa makamashin man fetur wanda yanzu duniya tace bata buƙata saboda matsalar sauyin yanayi idan kunne ya ji, to jiki ya tsira, kuma gwamnatin ka zata kafa tarihi wanda zai haifar da ɗa mai ido.
