Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Wannan mako shi ne na karshe cikin wannan shekara ta Miladiyya ta 2023, ga masu nisan kwana. Cikin yardar Allah mai kowa mai komai, mun kasance cikin masu rai da lafiya da suka ga wannan shekara. Da fatan Allah zai ja kwanakinmu mu ga shekara mai zuwa cikin rayayyu.
Abubuwa da dama sun faru da za su dade a zukatan ’yan Nijeriya, na dadi da akasin haka, wadanda za a yi ta tunawa da su, saboda tasirinsu a rayuwarmu. Kama daga shirye-shiryen Babban Zaven 2023 da kafa sabuwar gwamnati, cire tallafin man fetur, tsadar rayuwa, hukuncin kotunan sauraron kararrakin zabe, sace-sacen ’yan makaranta, shari’ar tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, da harin bam kan masu Maulidi a Tudun Biri da ke Jihar Kaduna, da kuma hare-haren ta’addanci a kauyukan Jihar Filato.
Babu abu mafi daukar hankali cikin wannan shekara ga ’yan Nijeriya kamar sanarwar janye tallafin mai fetur, wanda har kawo yanzu da nake rubutun nan tasirin cire tallafin man na cigaba da jefa rayuwar ’yan kasa cikin garari da jidali. Sai kuma yadda ’yan fashin daji masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, suka addabi manyan makarantu da satar dalibai, musamman dalibai mata.
An rawaito cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba na shekarar 2023 an sace dalibai akalla 204 daga makarantu daban-daban da ke arewacin kasar nan a hare-haren ’yan bindiga 16. A tsakanin makwanni uku kadai an sace dalibai daga manyan makarantun kasar nan da suka tayar da hankalin iyaye da sauran ’yan kasa, ciki har da sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
A ranar 3 ga watan Satumba, ’yan bindiga sun kai hari Jami’ar Tarayya da ke Gusau, inda suka sace dalibai 24. Kodayake daga bisani an ce jami’an tsaro sun bi bayansu sun ceto 13 daga cikinsu. Bayan sati biyu kuma sai ga rahoton sace wasu dalibai 5 daga Jami’ar Tarayya ta Dutsinma a Jihar Katsina. A ranar 10 ga watan Oktoba kuma aka sace dalibai 4 daga Jami’ar Jihar Nasarawa.
Duk wadannan sace-sacen sun faru ne a tsakanin kwanaki 19, abin da ya kara daga hankalin ‘yan Nijeriya duba da irin yadda aka samu kai na tsadar rayuwa, da rashin tsaro a kasa. A nan qasa zan kawo adadin wasu sace-sacen dalibai da suka auku cikin shekarar da ta gabata don ku fahimci tasiri da yawaitar matsalar a cikin wannan shekara ta 2023.
A ranar 20 ga watan Janairu an sace wasu ’yan makarantar firamare su 6, a Karamar Hukumar Doma da ke Jihar Nasarawa. A ranar 2 ga watan Afrilu, ’yan bindiga sun sace wasu dalibai 2 a Karamar Hukumar Bunguɗu, ta Jihar Zamfara. Haka nan a kauyen Awon na Ƙaramar Hukumar Kachia da ke Jihar Kaduna an sace dalibai 8 daga wata makarantar sakandiren gwamnati (GSS Awon), tare da wasu mutanen gari.
An kuma sace dalibai 10 daga wata makarantar sakandiren gwamnati da ke Kaduna, a ranar 4 ga watan Afrilu. A ranar 21 ga watan Afrilu a Jihar Inugu ma an sace wani dalibi a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Inugu.
A ranar 14 ga watan Yuni ’yan bindiga sun sace wasu daliban Jami’ar Jos su 7 a ranar 14 ga watan Yuni. A Karamar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna an sace dalibai 7 da malami daya a wata makarantar sakandire. Ga kuma daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau da na yi magana a baya, su 24 da aka sace a ranar 22 ga watan Satumba.
Ranar 26 ga watan Satumba kuma an dauke wata daliba daga Jami’ar Isa Mustapha Agwai da ke Lafia a Jihar Nasarawa. Ga kuma daliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma su 5 da aka dauka a ranar 4 ga watan Oktoba. Aka kuma sake sace wasu daliban Jihar Nasarawa su 4 a ranar 10 ga watan Oktoba.
Wadannan bayanai ne da aka samo su daga bayanan da aka tattaro daga wajen jami’an tsaro da ’yan jarida game da sace-sacen da aka riqa yi wa dalibai a sassa daban daban na kasar nan. Kuma wannan kididdiga ba ta hada da sauran mutane gama-gari da ake daukewa ba dare ba rana.
Tun daga watan Afrilu na shekarar 2014 da ’yan ta’addan Boko Haram suka sace ’yan matan Chibok su 276 daga makarantarsu a Jihar Borno, ake cigaba da satar dalibai ‘yan makaranta, da yin garkuwa da su don karvar kudin fansa wanda aka ce suna amfani da kudaden wajen sayen makamai, don cigaba da ta’addancin da suke yi. Ban da sauran hare-haren da ake kai wa a kauyuka da gidajen wadanda ba su ji ba ba su gani ba ana kashe na kashewa ana sace na sacewa.
A wasu rahotannin da ake bayarwa ma har bautar da irin wadannan mutane da ake sacewa ake yi, ana sa su aikin wahala, irinsu aikin noma ko hakar ma’adinai a cikin dazuka. Yayin da ake tilastawa mata daga ciki auren ’yan bindiga, ko amfani da su ta karfi, ma’ana a yi musu fyade. Subhanallah!
A daya bangaren kuma cire tallafin man fetur ya jefa rayuwar jama’a cikin wani mawuyacin hali, tsadar abinci da sauran kayan masarufi, da tsadar kudin mota, da hauhawar farashin kusan kowanne abu na rayuwa. Duk da yake gwamnati ta ce za ta raba tallafi ga talakawa da samar da matakan rage radadin talauci. Amma har kawo yanzu jihohi qalilan ne suka yi wani abin a zo a gani, sauran jihohin kuwa sun bi kan kudaden da gwamnatin tarayya ta bayar Naira Biliyan 20 ga kowacce jiha zuwa wasu harkokin na daban.
Rahotanni ma sun nuna a wasu jihohin kashe mu raba aka yi tsakanin gwamnati da ‘yan kwangilar da aka bai wa alhakin kawo abincin da ake rabawa talakawa, inda ake raba shinkafa marar kyau, ko dadadden abincin da ya fara lalacewa. Shi din ma ba yadda ya kamata ake rabawa ba, don wasu mudu-mudu ake ba su, wasu kuma iya ’yan wata jam’iyya kawai ake bai wa tallafin, wadanda ba sa jam’iyya mai mulki kuma ko oho.
Lallai ya kamata a shekarar da za mu shiga gwamnati ta kara dagewa don ganin ta cika alkawuran da ta yi wa ’yan Nijeriya ba irin romon bakan da aka saba yi mana ba. Kuma lallai a samar da ingantattun matakan tsaro, don kare makarantun da yaranmu ke karatu a ciki, da sauran jama’a matafiya da na cikin gari.
Muna fatan shekarar 2024 ta kasance mai albarka da karuwar arziki, zaman lafiya da ingantaccen tsaro, a dukkan fadin kasar nan. Amin
