Tare da BASHIR MUDI YAKASAI
Mun yi bankwana da shekara ta 2023, shekarar da duk dan Nijeriya ba zai mantata ba Saboda tsanani da kuncin rayuwa na rashin kudade a hannun jama’a ga kuma tsada da hauhawar farashi na fatara da kuma zama cikin zulumi saboda masu kai hare-hare domin kama mutane domin yin garkuwa da su, sai amfanshesu da madukun Kudade, amma Idan bah aka ba kai da dan uwanka sai a Darul-Salam, wato Lahira.
To, Alhamdulillah, Allah ya nuna mana wannan Shekara ta 2024, Saboda haka muke yi mata maraba lale da fatan Allah ya kawo mana dauki da alheransa, kamar yadda muka sani komai nisan jifa, wata rana kasa zai fado. Kamar yadda muka sani, Nijeriya kasace da Allah ya albarkace ta da abubuwa na alherai da bai yi wa kasashe da muke jin amman su a wannan sarari na maliki yaumiddeeni. Kasa ce mai ni’imar gaske ga filayen noma, babu wani fili kafa daya da bana nom aba ko kiwo.
Amma Saboda halayenmu na rashin kirki haka ‘yan Nijeriya sama da Kashi Arba’in (40%) cikin dari (100) suke kwana da yunwa. Kuma Allah ya albarkaci kasar da al’umma sama da miliyan biyu da dubu dari uku, amma sama da rabi, dukkan ‘yan sha ka tafi, babu kishin zuci balle kishin kasa.
Nijeriya Allah ya albarkace ta da makamashin man fetur, it ace ta Shida (6) a duk fadin duniya da take iya fitar da gangar danyan man fetur (Grude Oil) Sama da ganga miliyan guda a rana. Kuma itace ta biyu (2) a duk fadin duniya wajan samar da Gas da yafi kowanne daraja. Bayan haka an tabbatar Nijeriya na gaba- gaba wajan kasashen da suke da mutane masu fasaha da kwarewa a fannin kimiya da fasaha da sha’anin kiwon lafiya (Scientists, technologists and medical practitioners). A harkar soja babu da na biyu a duk fadin Afirka.
Amma abin takai ci, Nijeriya ba ta iya ko tsinken Sakatar hakori sai an kawo mata daga birnin sin, wato China. Kafin zuwan turawan Birtaniya da Portugal da Farans har da Jamus, har kasar Birtaniya ta kafa tutarta ta mulkin mallaka A Shekara ta 1908 kasashen Arewa kamar Kano, Katsina, Daura, Sokoto, Damagaran, Maradi da dai sauran su inda suke gudanar da sana’o’in su tun daga kere-kere, da Saka da Jima da Dukanci da kiwo da sun a kamun kifi, amma yan zu duk da miliyoyin daloli da suke shugowa qasar har yanzu babu wutar lantarki Ishasshiya, babu ruwan sh, babu hanyoyi. Babu ta zama a bakin kowa.
Tanbayar ita ce me yake janwo koma baya na al’umma a fannin ci gaba wajan gina kasa da gina ‘yan kasa wato ‘Human development’. Babban matsalar itace cin hanci da rashawa da sata da biro, wato al’kalami inda mutum zai sa alkalamin sa ya kwashi biliyoyin daloli suke kasashen da suke ikirarin su masu bin tsarin akidar damokaradiya, tsari da yake yaqi da zalinci da azzalimai, sai suka zama masu daure gindin sace-sace a duk fadin duniya domin su giina kasashen su.
Su duniya take kira da barayin zaune Amurka da dukkan kasashen Yammacin turai-Birtaniya, Faransa, Potugal, Jamus, Italiya da dai sauran. Duk ginin da ka gani ko hanya ta karkashin kasa ko ta sama da hanyoyin Jiragen kasa ko na ruwa. Mai karatu gaskiyar Magana duk ci gaban da ka gani a Amurka ko a Yammacin sun samu ne daga dukiyar Afirka da kasashen Asiya da kuma Latin Amurka. Tun daga lokacin cinikin bayi zuwa mulkin mallaka da kuma yan zu na sabon fasalin mulkin mallaka-(Neo-Colonialism) wato ci da gumin wani. To, ina mafuta?
Mafuta ita ce fita daga Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da duk wasu tsare-tsare ta na Bankin Duniya, da Asusun Lamini na Duniya (IMF) da UNESCO da WHO da UNICEF, kai da duk wata mu’amula da aka ce ta majalisar Dinkin Duniya ne. Domin ba wani abu bane illah hodar Ibilis, duk wanda ya shiga ya fada rijiya goba dubu ba kai ba fita, sai yadda suka yi da kai ta fuskar tattalin arziki ko Siyasa koma ta zamantakewar jama’ar ka. Sai kuma su kawo wata gubar da sunan damokaradiya su raba ku gida-gida har kasha goma sha uku (13) da sunan ‘Fundamental Right?
Saboda haka idan har muna so mu ci albarkacin da Allah yayi wa wannan qasa na makamashi man fetur da Gas da suaran ma’adinai kamar yadda kullum muke fada kamar kuza (tin), Tma (Columbite), Bakin Karfe (Iron Ore), Kwal (Coal), Dutsan wuta (Limestone), Darma (Lead), Kwano (Zinc), kai sai a cika wannan takarda da sunan ma’adinan da Nijeriya take da su wadan da suke kawo biliyoyin daloli ga kasa, amma suke zurarewa zuwa wadancan kasashe. Kana yin Magana kazama abokin gabarsu, sunan ka dan Ta’adda.
Wannan gata da Allah yayi mana na dukiya da tarin jama’a ya mayar da mu babbar kasuwa, masu kuwa zuba jari su ka kuwa kunno kai a shekara 1960 da 1970 har zuwa farko-farkon 1980, lokacin da Naira take kanshin Dan goma, inda take gogaiya da fam ta ingila da Dala ta Amurka inda kuma ta sha gaban Saifa ta Faransa tayiwa Riyal na Saudiya fintinkau, da naira dari zaka yi cefanan gidan ka har da kashin miya kai da mai dakin ka da ‘ya’yan ku uku (3) da kuma bakin ku biyu magidanta.
Noma kuwa a wancan lokaci, lokacin da berayan ba su girma ba sun kai girman beran dinka, Nijeriya na kan gaba a Afirka a noman kwarar manja, auduga kuma gamu da fata da Kirgi ga kuma gyada. Kamar yadda muka ce ga kuma Sana’o’in hannu, kusan kasha saba’in (70%) cikin dari na kowanne gida suna da sana’arsu ta gado kuma suna yenta ka’in da na’in saboda da rawar da muke takawa Afirka muna ciyar da kanmu kuma mu ciyar da wasu ake yi mana kirari da “Giant of Africa”. Wato Toron Giwar Afirka.
Daga lokacin muka rungumi tsarin damokaradiya a shekara ta 1999 yan zu ne kan gaba a hali na Allah wadai ‘yan Takardarmu (Elite) Madam Diezani Alison Maduke da Mista Godwin Emefiele da Alhaji Ahmad Idris da kuma Malam Mele Kyare da Daraktocinsa sama da goma sun wawuri sama da naira tiriliyon goma sha biyu (12T). Mun kawo wadannan ne a matsayin misali. Saboda kazantar satar da suke yi, wato ‘yan Takardar (Elite) na Nijeriya, a shekarun baya shugabar EFCC, Uwar Gida, Madam Farida M. Waziri take cewa, “ya kamata a riqa bincikar kwakwalan ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa, saboda halin sata da cin amanar dukiyar kasa ya fuce hankali ga duk mai hankali.
Siyasar damokaradiya babu abin da ta samar illa dandalin Kyankyashe beraye da gafiyoyi da kuraye har da zakuna mavarnata na gaske. Ana kuma faraway tun daga Kansuloli su 8,810 ‘yan kuci ku bamu, zuwa Shugabannin kananan hukumomi su 774 da ‘yan majalasar jiha su 990. Ga kuma ‘yan majilasar, wakilai su 360 da Sanatoci su 109, baya ga gwamnoni da mataimakansu su 72. Sai babban zaki Shugaban kasa da mataimakinsa. Idan kafara wadannan azzalimai su dubu goma sha daya da dari daya da goma sha bakwai (11, 1117), wanda duk bayan shekara hudu (4), zai koma kan kujerarsa ya ci gaba da linkaya cikkin tafkin dukiya kasa.
Mai karatu, ba mu yi bayani na ministoci ba da kwamishinoni ba da masu bayar da shawara da masu taimakawa da kuma masu taimakawa na musamman, wadanda ake kira da “rasa kunya berayen masallaci” domin barnar da suke yi ta kusa fi ta iyayen gidansu, domin sune kannikan farauta a kwangilolin cikin gida da na waje. Idan kaji wata ba da kalar a tsakanin su har kai wa take ga kisa, ko kuma tona asiri.
Saboda lokaci, za mu tsaya a nan ba don komai ba sai tarin shawarwari da muke da su SHUGABAN QASA Chief Asiwaju Ahmed Bola Tinubu da Mataimakinsa Malam Kashim Shatima Mustapha Saboda dukkan su yi Imani da abu daya da tashin kiyama wato ranar Sakamako da kuma wuta da Aljanna ta Shugabanni. To, Alhamdulillah, wannan Shekara da muke maraba da ita (2024), Shekara ce ta warware tsakani kaba da Abawa, wato tsakanin barayin zaune da kuma barayi musa lasisi a masana’artar makamashi da masana’artar ma’adinai a wannan kasarmu ta Nijeriya. Mun gode a biyo sannu a hankali.
