Hatta ƙanzo ma ya yi tsada

Spread the love

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ɗan Nijeriya ba ya buƙatar wani zurfin ilimi wajen fahimtar yanda tattalin arzikin Nijeriya da ma wasu hasashen duniya ya samu koma baya. Ƙasashen ba sai can wata nahiyar ba daga ma makwabta za a iya fahimtar yadda rayuwa ta yi tsada. Mun duba yadda gabanin janye takunkumin ECOWAS kan jamhuriyar Nijar a ka samu matsala gwamnatin Niamey da talakawa ke ta kuka har ta kai ga shigar da kara kotun ECOWAS a Abuja.

Mu tuna yadda rufe iyakokin Nijeriya na ƙasa zamanin tsohuwar gwamnatin Buhari ya jawo tsadar kayan abinci musamman shinkafa duk da yadda a ke noma ta a cikin gida. Mazauna yankunan kan iyaka za su baiyana yadda ƙananan sana’o’in su su ka taɓu. Shin ina bakin zaren ne ko dai shikenan haka rayuwar za ta cigaba da gudana? Kai tsaye an san cewa mafi tsadar rayuwa da ta ke wahalar da ‘yan Nijeriya ta baya-bayan nan ta faro ne daga ranar 29 ga watan Mayun bara bayan jawabin farko na shugaba Tinubu da ya janye dukkan tallafin man fetur.

Gaskiya ban ga laifin sa a lokacin kai tsaye na don ban hango azabar za ta shafi hatta ƙanzon kasan tukunya ba. Ba fa Tinubu ba ne kaɗai ke da wannan muradi a zaɓen na 2023. Ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar da na jam’iyyar LEBA Peter Obi sun nuna muradin janye tallafin in sun haye karagar mulki. In duk manyan ‘yan takara sun bayyana rashin son tallafin man fetur ba hakan na nuna kai tsaye tallafin ba shi da amfani ba ne.

Zai yiwu gwamnati za ta fi son tura kuɗin wasu sassa da za a share shekaru ba a ga amfanin hakan ba ko ma ba mamaki wasu ma daga ‘yan Nijeriya da ke raye a yanzu sai rai ya yi halin sa kafin a fara ganin amfanin matakin. A gefen talakawa kuwa ai tallafin nan ya kuwa taimaka wajen samar da saukin rayuwa duk da bayanan ai a baya wasu tsiraru ne ke amfana da tallafin. Wallahi na ji ko na ga talakawa na cewa ashe su ne tsirarun da a ke nufi.

Kusan kullum kayan masarufi sai ƙara tsada su ke yi a kasuwannin Nijeriya.

A zahiri duk mai shiga kasuwa zai ga cewa kaya na kara tsada kusan duk lokacin da mutum ya sake komawa don sayan abun da ya saya jiya ko shekaranjiya.

Wato yanayin tashin farashin na da ban mamaki kuma ya danganta daga wajen diloli zuwa wajen ‘yan sari da masu shigar da kayan lunguna.

A tsakanin dila daga kasuwa a gari ɗaya a kan iya samun bambancin Naira 400 zuwa 500 a lunguna.

Duk da labarun da ba su da tabbas na raguwar farashin dala ba wani sauyi da hakan ya yi kan farashin kaya.

A na su ɓangare ‘yan kasuwar mai kan ƙara farashin lita duk lokacin da su ka so yin hakan a tsarin kasuwa ta yi halin ta.

Babban bankin Nijeriya CBN ya ɗauki matsayar dawo da sayarwa kasuwar canji dala bayan dakatar da hakan tun mulkin tsohon shugaba Buhari.

Bankin ya ce kowane mai kamfanin canjin kuɗi zai iya samun dala 20,000 bayan ajiyar kuɗi da bankin.

Kazalika bankin ya kafa ƙa’idar sayar da dalar kan Naira 1,301 ga ‘yan canjin da ba su damar kara kashi 1% na farashin.

Hakanan bankin ya ce ya zama wajibi dukkan masu canjin su buga allon farashin canji a ofisoshin su da kuma yin bayanin yadda su ka tafiyar da canjin kullum a wata manhaja.
Gwamnan bankin Olayemi Cardoso ya ce sam ba shi da hannu wajen rikicewar tattalin arzikin Nijeriya.

A na ta ɓangare Majalisar Dattawan Nijeriya za ta binciki yadda tsohuwar gwamnatin Buhari ta karɓi zunzurutun kuɗi Naira tiriliyan 30 daga babban banki CBN ƙarƙashin jagorancin Godwin Emefiele.

Mataimakin shugaban majalisar Barau Jibrin da ya jagoranci zaman majalisar ya ce karɓar kuɗin ta hanya – hanya na daga dalilan tashin farashi a Nijeriya.

Majalisar ta kafa kwamiti mai mutum 9 don gudanar da bincike kan yadda a ka sarrafa kuɗin da dawo da rahoto cikin mako biyu.

Jibrin ya ce irin kuɗin dai ba a maidawa bankin ba don haka za su cigaba da zama bashi a kundin bayanan bankin. Ba mamaki hakan na nuna za a cigaba da waiwaye kan ayyukan da tsohuwar gwamnatin Buhari ta aiwatar inda tsohon gwamnan babban banki Emefiele ke tsakiyar tuhuma ta wawure maƙudan kuɗin da sun sabawa hankali a ƙarƙashin kulawar gwamnati mai tutiyar yaƙi da cin hanci da rashawa amma sai masu dokar barci su ke buge da gangyaɗi.

A wuni na biyu haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta dakatar da zanga-zangar nuna damuwa ga tsananin tsadar rayuwa a Nijeriya.

Dama zanga-zangar ta wuni biyu ce wato Talata da Larabar da su ka gabata.

Membobin ƙungiyar wato ma’aikata a dukkan matakai a faɗin Nijeriya da sauran ƙungiyoyin farar hula sun shiga zanga-zangar kama daga Legas a kuryar kudu maso yammacin Nijeriya zuwa Gombe da sauran sassa a arewa maso gabas.

Ma’aikatan ɗauke da kwalaye na nuna takaicin tsada da a ke ciki sun zaga sassan da za a saurari ƙorafin da gabatar da jawabai da waƙoƙin gwagwarmaya na ma’aikata.

A Abuja tawagar ƙwadagon ƙarƙashin Komred Joe Ajaero ta shiga har cikin harabar majalisar dokoki don isar da saƙon buƙatar kawowa talakawa ɗaukin gaggawa ta hanyar sauya manufofin gwamnatin Tinubu da su ka yi hannun riga da kyautata rayuwar al’ummar ƙasa.

Aƙalla dai an samu wani gungun jama’ar da ba ‘yan ƙwadago ba da su ka fito don nuna mara baya ga manufofin gwamnatin.

Ƙungiyar ta ba da wa’adin mako biyu ga gwamnatin ta aiwatar da yarjejeniyar da a ka yi da ita kan kawo sauƙi inda daga nan za su zauna don ɗaukar mataki na gaba.

Tun gabanin fara zanga-zangar ƙungiyar ƙwadagon ta gargaɗi gwamnati da cewa matuƙar ta sanya wasu zauna gari banza su ka kai ma ta hari a zanga-zangar to za ta shiga yajin aikin da komai zai tsaya cak a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar Komred Joe Ajaero ya yi zargin gwamnati ta tsara wani gungu a gaggauce don kai farmaki kan zanga-zangar lumana da za su gudanar.

A martanin gwamnatin ta bakin mai ba wa shugaba Tinubu shawara kan sadarwa Bayo Onanuga ta musanta ikirarin da nuna jita-jita ne kawai.

Manyan malaman Islama a Nijeriya sun buƙaci ƙungiyar ƙwadago ta janye zanga-zangar da ta shirya don nuna damuwa kan tsadar rayuwa.

Shugaban majalisar shari’ar Islama a Nijeriya Malam Nafi’u Baba Ahmed ya ce a tarihi zanga-zanga ba ta haifar da sakamako mai kyau.

Baba Ahmed ya buƙaci ƙungiyar qwadago ta vullo da wata hanya da ta sha bamban da zanga-zanga don muradun zaman lafiya da hana keta doka da oda.

Shi ma shugaban majalisar gudanarwa ta Izala mai helkwata a Jos Sheikh Nasiru Abdulmuhyi ya ce haƙiƙa mutane na cikin wahala amma zanga-zangar ƙwadago ba za ta samar da maslaha ba.

Sheikh Abdulhmuhyi ya yi kira ga gwamnati ta ƙara buɗe rumbunan abinci don tallafawa jama’a; ya na mai buƙatar ƙungiyar ƙwadago ta fi maida hankali wajen tattaunawa.

Shugaban ƙungiyar kwadago ta NLC Komred Joe Ajaero ya ce ba wanda zai hana su zanga-zangar lumana, ya na mai zargin gwamnati da haɗa gungun zauna gari banza wajen kawo tashintashina a lokacin zanga-zangar.

Gwamnatin Nijeriya ta shugaba Tinubu ta ɗauki matakin amincewa da aiwatar da rahoton Stephen Oronsaye da ke ba da shawarar tsuke gwamnati.

Majalisar zartarwa ta amince da aiwatar da rahoton don rage kashe maƙudan kuɗi a lamuran gwamnatin.

Rahoton dai na Oronsaye ya fito shekaru 12 da su ka wuce inda kuma bayan shekaru biyu a ka fitar da takardar amincewa da rahoton.
Ministan labaru Muhammad Idris ya ce an kafa kwamiti don aiwatar da matakin da zai soke wasu ma’aikatu da sassan gwamnati da kuma haɗe wasu.

Idris ya ce hakan ba ya na nufin sallamar ma’aikata daga aiki ba ne amma sai don rage tsadar aiwatar da lamuran gwamnati. Za a zuba ido don ganin yanda hakan zai yi tasiri ba tare da shafar yawan ma’aikata ba.

Kammalawa;

Gaskiyar magana talakawa da ma masu matsakaita wajen samun kuɗin shiga na jin jiki a tsadar rayuwa. Babbar matsalar ita ce wadatar abinci. Hatta batun buɗe rumbunan abinci don tallafawa jama’a na da zummar rage tsadar abincin ne a kasuwa. Wato ma’ana ai gwamnatin ba za ta iya raba abinci kyauta a ce kowa zai wadata ba.

Gwamnatin ya dace ta sani matuƙar mutane na jin yunwa to haƙurin da a ke cewa su yi don gobe za ta yi kyau zai yi wuya. A tattara bayanai daga ‘yan ƙasa za a gane mutane na cikin matuƙar ƙunci da ya zama mai muhimmanci a kawo matakai na kusa da za su rage zafin damuwar. Gwamnati ta dau matakan duba yadda farashin kayan masarufi ke cigaba da zama a tashe ko da bayan an kawo batun saukar dala. A hana cin kazamar riba don gujewa ƙazamin sakamako!

By Editor