Wasu sanannu ke ba yan ta’adda kariya- Gwamnan Zamfara

Spread the love

Gwamnan Jihar Zamfara ya zargi wasu sanannun yan Najeriya da taimakawa wajen sakin wasu yan ta’adda waɗanda suka amsa laifukansu na kisan kai.

Gwamnan ya nuna rashin jin daɗi bayan da ya samu labarin wasu masu ƙarfi a gwamnati sun taimaka wajen bada belin yan ta’addan.

Gwamnan na wannan bayanin ne a ma’aikatar sharia ta Jihar Zamfara, inda yake cewa wasu yan ta’adda da gwamnatin shi ta kama, ya samu labarin kotun da ke Abuja ta bada belin su.

Yan ta’addan su amsa laifukan su na kisan kai, da kuma makamai da aka kama su dashi. Amma hakan bai hana kotun da ke Abuja ta bada belin su ba kamar yadda labarin ya zo mashi jiya.

By ukarofi