Al’ummar ƙauyen Kuruma na neman agajin gwamnatin Kano kan mutuwar mata a haɗarin jirgin ruwa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Mutanan ƙauyen Kuruma a ƙaramar Hukumar Bunkure da ke Kudancin Kano, na neman agajin gaggawa sakamakon mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya halaka mata huɗu a yayin da suke ƙoƙarin zuwa aiki domin dogaro da kansu da kuma tallafawa iyalansu a wannan yanayi.

Matan waɗanda suka rasa ransu a ƙoƙarin sauka jirgin ruwan ne sakamakon rashin kyakyawan wuri da jirgin ruwan zai tsaya su sauka, hakan ta sa jirgin ruwan da ake kira Komi ya hantsila inda mata huɗu ciki har da ‘ya’yan mace ɗaya da ake kira Maryam da Magajiya da suna cikin mata huɗun da suka rasa ransu a wannan ƙauye na Kuruma da ke ƙaramar hukumar Bunkure.

A jawabinsa ɗaya daga cikin shugabanin ƙauyen mai Unguwa Muhammad Yahuza, ya ce dole ce ta ke sasu shiga wannan jirgin ruwa da kuma sauka da ake yi ta hanyar tsallaka fita don haka suna kira ga Shugaban ƙaramar hukumar Bunkure da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, da sauran ƙungiyoyin jinƙai na Kano da ma duniya baki ɗaya kan su kawo musu agaji na kawar da wannan matsala da ta yi sanadiyyar rasuwar ‘ya’yansu mata huɗu rigis a wannan ƙauye na Kuroma a ƙaramar hukumar Bunkure.

By ukarofi