Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
An bayyana cewa babban kuskure ne da al’umma ke yi a wannan lokaci na goyan bayan zaluntar wani ɗan jam’iyya da ba taka ba ko kuma zaluntar wani saboda saɓanin ra’ayi akan dukkan wani abun domin duk wanda ya goyi bayan zalintar wani kan saɓanin jam’iyya ko saɓanin ra’ayi ya karya ƙa’idar kyakkyawar mu’amala da kuma ƙa’idar addini, domin babu wani addini da zai goyi bayan zalunci ballantana saɓanin ra’ayi ko na jam’iyya ko na ra’ayi ya sa kaji daɗi wannan da daidai ba ne, don haka al’umma ta guji wannan mummunar fahimta da wasu suke da ita na jin daɗi idan an zalunci wanda ba ɗan ƙungiyarka ba, ko ba ɗan jam’iyyar ka ba, ko ba ɗan ra’ayin ka ba, domin tausayi da ƙaunar juna da yin adalci a zuciya da sarari shi ne babban abun da ke kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma a kowana lokaci kamar dai yadda ɗaya daga cikin masu fashin baƙin da nazarce nazarce a kafofin sadarwa Khalifa Alhaji Murtala Mai Sallah ya bayyana a wannan lokaci.
Haka kuma ya bayyana ta takaicinsa akan yadda ‘yan siyasar Nijeriya suke wa dimukuraɗiyya karan tsaye da kama karya ba tare da jin tsoro ko kunya ba wanda shi ma wannan kuskure ne babba, inda ya ba da misali da abun da ke faruwa a jihar Ribas da sauran wurare wanda ya kamata shugabanni, su ji tsoron Allah su yi adarci a kan duk kanin wani al’amari da ya shafi al’umma wanda hakan babbar hanya ce ta kawo zaman Lafiya, cigaba, Tsaro, da kwanciyar hankali da sauransu a ƙasa baki ɗaya.
A ƙarshe Khalifa Alhaji Murtala Mai Sallah ya nuna damuwa a kan yadda wasu wakilai ko wasu shugabannin siyasa ke wawantar da mutanan sun a rashin taɓuka komai wajan fannin Ilimi, Lafiya, sana’o’I, kasuwanci, Noma da sauransu ta yadda su ka mai da mutane kamar ba su san abin da su ke yi ba, ta yadda sai dai kawai a kawo muku tallafin abinci da kuɗi a shekara, sakamakon matsin rayuwa da al’umma ta samu kanta sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci da rashin sanin ya kamata da kuma rashin tsoron Allah wanda ya kamar kowa ya tashi yayi aiki na gari a ƙashin kansa, kuma ya yi addu’ar neman dai dai to da samun kyakkyawan shugabanci a wannan ƙasa.
