Daga UMAR GARBA a Katsina
Tsohon daraktan hukumar yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (rtd), wanda ya kwashe sama da watanni biyu a hannun ‘yan ta’adda, ya bayyana wahalar da ya sha a hannun ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane.
Tsiga ya bayyana cewa an tsare shi tare da sauran mutanen da aka sace a wani daji da ke kewaye da tsaunuka, cike da dabbobi masu haɗarin gaske.
Ya bayyana tsira da ransa da yayi inda ya ce ba komai bane illa ɗauki da Allah ya kawo masa.
Tsiga mai shekaru 72 ya ce: “An tsare mu wuri ɗaya da dabbobi masu haɗari irinsu kuraye, macizai, da kunamai, kwana ɗaya kafin a sake ni, jiya da safe, lokacin da nake zaune kan wani dutse, kwatsam sai muka ga wata kura na ta zagaya mu, tana neman abinci. To wane irin abinci ne? Mu ne ’yan adam.”
“A tsawon lokacin da muka yi a can, muna zaune tare da macizai da kunamai, amma abin da ya fi ban tsoro shi ne yadda suka bi da mu, mu da muka riƙe muƙaman soji, duk lokacin da sojoji suka kai musu hari, sai su fito da mu, su yi amfani da mu a matsayin garkuwarsu, sun so su kashe mu a cikin hari ta sama da sojoji ke kai musu”.
Tsiga ya ci gaba da ba da labarin wani yanayi mai ban tsoro da ya fuskanta a lokacin da yake tsare a hannun ‘yan bindingar wanda ya shafi harin makamin roka da sojoji suka jefa a sansanin ‘yan ta’addar amma makamin bai fashe ba.
Ya ce: “Lokacin da aka kai harin, an harba roka kan ‘yan ta’addan, amma bai fashe ba, sai suka ɗauki rokar da ba ta fashe ba, suka ajiye shi a inda nake barci, suka ɓoye ta hanyar da idan na taɓa shi zai tashi, amma na tsira sanadiyyar rahamar Ubangiji.”
Da yake magana a madadin sauran mutane 18 da aka ceto, Tsiga ya miƙa godiyarsa ga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribaɗu, da kuma babban hafsan tsaro na ƙasa.
