Gurɓacewar muhalli da tasirinsa ga cigaban ɗan Adam

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A lokacin rubuta wannan maƙala, adadin mutanen da suka rasa rayukansu a garin Mokwa na Jihar Neja, sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da aka yi a garin, ya haura 200. Yayin da sauran al’ummar garin ke cigaba da ƙirga yawan asarar da suka yi ta dukiya da sauran abubuwan amfani. Da fatan ubangiji Allah zai mayar musu da ninkin abin da suka rasa, ya kuma basu haƙuri da juriyar rashin ’yan uwansu da suka yi.

Ambaliyar ruwa na daga ibtila’i mafi muni da ke shafar ɗan adam da muhallinsa, wanda bayan asarar rayuka, amfanin gona da dukiyoyi, akwai kuma batun yaɗuwar cututtuka, saboda cakuɗuwar ƙazanta da abubuwan amfani. Sannan akwai yiwuwar fuskantar ruftawar gine-gine da zabtarewar ƙasa. Cikar manyan rafuka, da gurɓacewar ruwan amfani da dagwalon ruwan ƙazanta mai datti.

Matsalar lalacewar muhalli abu ne da yanzu duniya ke fuskanta, cikin ƙunci da takaici, sakamakon yadda rayuwar ɗan adam ta samu kanta a cikin ƙalubalen muhalli da duniya ta samu kanta a ciki. ƙaruwar zafin rana da saurin janyewar ruwan sama, da bushewar ƙasa, kwararar hamada da ita kanta ambaliya da ke jawo asara mai yawa.

A yayin da duniya ke bikin Ranar Muhalli ta Duniya na wannan shekara, wanda ke mayar da hankali kan yadda ake cigaba da samun gurɓacewar muhalli ta dalilin sharar robobin da ake amfani da su a matsayin mazubi don zuba lemo da ruwa, ko wasu abubuwa na sha da ake sarrafawa, domin kashe ƙishi. Ana ganin yawan sharar robobin da ake zubarwa a bola da magudanun ruwa na haifar da barazana ga muhalli. Kuma hakan harwayau, yana taimakawa cushewar magudanun ruwa da ke haifar da ambaliya. Kamar yadda muka sani robobin ba sa narkewa, ko motsewa su bi ruwa.

Bincike ya nuna cewa, an samu ƙaruwar kamfanonin sarrafa lemon kwalba da ke amfani da robobi wajen zuba nau’in kayan shaye-shaye na marmari da suke yi, har da ninki huɗu, a cikin fiye da shekaru 30 da suka gabata. An gano ana sarrafa irin waɗannan robobi fiye da ton Miliyan 500 a duniya. Kamar yadda muka sani ana sarrafa waɗannan robobi ne daga sinadarin ɗanyen man fetur da gas, waɗanda a karan kansu suke matsayin guba ga muhalli.

Wani abu da yake ɗaga hankalin masana muhalli shi ne yadda za a tsaftace muhalli da rafuka da teku daga dagwalon sharar robobi, domin a sake sarrafa robobin zuwa wasu abubuwan amfani, ko kuma a sake tsaftace robobin a cigaba da amfani da su a matsayin mazubi don sayar da ruwa ko wasu nau’ikan abin sha, irin su kunun zaƙi, zoɓo, ruwan lemo ko tsamiya, wanda jama’a ke saya su sha don kashe ƙishin ruwa.

Kodayake muna iya gani a biranen mu yadda sabuwar harkar jari bola ta ɓangaren robobi ke samun karɓuwa a jihohin ƙasar nan. Muna ganin yadda yara da matasa ke bin bola da gidajen al’umma ko wuraren taruka suna kwashe robobin da ake zubarwa, domin zuwa su sayar su samu kuɗin kashewa. Haka suma masu saye daga wajen masu harkar jari bola, ko gwalagwas a wasu wuraren, suna samun kuɗaɗe masu yawa. Domin a wajen su ne masu kamfanoni ko dillalan dake kai wa kamfanoni a sake sarrafawa, ke saye don a sake juya robobin zuwa wasu abubuwan amfani.

Fatima Aliyu Inuwa, wata mata ce mai sana’ar sayar da kayan ruwan sanyi, irin su kunun zaƙi da zoɓo, wanda jama’a musamman leburori da ma’aikata ke saya don su kashe ƙishi, ta bayyana cewa tana sayen robobin ne daga wajen masu bola jari da ke tarawa suna sayarwa. Sannan tana sa yara suna zagawa wuraren taruwar jama’a suna kwaso mata robobin tana biyan su, domin ta samu mazubin da za ta zuba abin sayarwarta a ciki.

Masu ƙananan sana’o’i irin na Malama Fatima, a cikin gidajen aure da kasuwanni, suna taimakawa wajen rage yawaitar robobin a tituna da cikin bola ko a magudanun ruwa. Sai dai hakan ba ya wadatarwa, lallai ne sai manyan ’yan kasuwa da masu masana’antu sun shiga cikin harkar yadda ya kamata, don a iya cin ƙarfin yawaitar robobi a cikin ruwa da kan tudu. Akwai abubuwa da dama da za a iya yi da waɗannan robobi a matsayin mazubi, ko abin ƙawata gidaje, da yin wasu abubuwa na amfani.

Wani bincike ya nuna cewa, akwai manyan dabbobin ruwa irin su kifayen dolphin fiye da dubu 300 dake mutuwa a teku duk shekara, sakamakon haɗiyar robobin da suke yi daga ruwa. Yayin da masana kimiyyar muhalli suka gano akwai robobin dake yawo a saman ruwa fiye da Tiriliyan 171 a manyan tekunan duniya. Don haka ake ganin idan ba a yi wani abu da wuri ba, yawaitar robobi a cikin ruwa zai cigaba da haifar da matsaloli ga duniya, ba kawai ga dabbobin da ke rayuwa a cikin ruwa ba, har ma da ɗan adam dake rayuwa akan tudu.

Yana da kyau masana kimiyya su gano wata hanya ta sarrafa mazubin da zai iya narkewa ko lalacewa da wuri a maimakon cigaba da sarrafa roba, wacce ba ta narkewa saboda daɗewa a ruwa ko a ƙarƙashin ƙasa. Lallai ne jama’a su haɗa hannu su ƙara faɗakar da juna muhimmancin kula da tsaftar muhalli, daga dagwalon shara da dattin robobi, da rage sayen abubuwan da aka zuba a robobi, kuma mu riƙa adana waɗanda muka yi amfani da su a gidajen mu domin sake amfani da su a matsayin mazubi.

Mu sani fa kula da tsaftar muhalli abu ne mai kyau, ba kawai ga cigaban kasuwancin mu kaɗai ba, har ma da lafiyarmu da rayuwarmu a bayan ƙasa. Lallai ne mu shiga cikin gangamin yaƙi da cigaba da sarrafa mazubin roba, da manyan kamfanonin duniya ke yi, domin rage yawan robobin da ke haifarwa muhallinmu illolin masu yawa. Musamman a yanzu da ake ƙara shiga lokacin damina, mu kaucewa barin robobi a hanya, saboda kada su cika magudanun ruwa da toshe kwata yadda za a iya samun ambaliya a unguwannin mu. Mu ƙarfafa gwiwar yaran mu wajen tsince robobi daga shara ko bola, domin kaiwa inda za a sake tsaftace su a yi amfani da su cikin aminci.

By ukarofi