Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar Social Democratic Party SDP, reshen Jihar Zamfara ta gargaɗi wani mutum mai suna Arc. Bilal Aliyu da ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar a jihar domin zaman lafiya da ci gaban jam’iyyar a jihar ko a hukunta shi.
Shugaban jam’iyyar na jiha Alh. Idris Abdullahi Bangaje ya yi wannan gargaɗin a wani taron manema labarai a Gusau yau Juma’a.
A cewarsa, shi ne halattaccen shugaban jam’iyyar da hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, hedikwatar jam’iyyar ta ƙasa, DSS, NSCDC da ofishin kwamishinan ‘yan sanda na jihar suka amince da shi.
Ya bayyana Arc. Bilal Aliyu da yake bayyana kan shi matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar a jihar, a matsayin yunƙurin siyasa na kawo rikici a jam’iyyar.
Alh. Bangaje ya ci gaba da cewa, jam’iyyar da ke ƙarƙashin sa ba za ta lamunta da irin wannan aika-aika ba, yana mai cewa za a bi duk matakan da suka dace don ganin jam’iyyar ta ci gaba da kasancewa dunƙulalliya.
“Za mu ɗauki dukkan matakan da suka dace a kan Arc. Bilal Aliyu wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar SDP na riƙon ƙwarya a Jihar Zamfara domin samun zaman lafiya da ci gaban jam’iyyar”. Yace
Alh. Abdullahi Bangaje, ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar SDP da magoya bayan jam’iyyar a jihar ta Zamfara da suci gaba da bin doka da oda tare da yin watsi da duk wani yunƙuri da ka iya kawo rarrabuwar kawuna da rikicin jam’iyyar a jihar.
