Tun da na hau mulki cin hanci ya zama tarihi a Nijeriya – Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa masu saka hannun jari na ƙasar Brazil cewa gyare-gyaren tattalin arzikin da ake aiwatarwa a Nijeriya suna samar da ingantattun sakamako, inda ya yi iƙirarin cewa “ba a sake samun cin hanci da rashawa ba” tun bayan da ya hau kujerar shugaban ƙasa.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Litinin tare da ministoci daga ƙasashen biyu da kuma mambobin ƙungiyar kasuwanci ta Brazil, inda ya sake jaddada shirye-shiryen Nijeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa a ɓangaren fasahar zamani, samar da abinci, masana’antu da makamashi.

Tinubu ya bayyana tattalin arzikin Nijeriya a matsayin “wata babbar kasuwa mai ɗimbin damammaki da kamfanonin Brazil ba su taɓa cin moriyarta ba.”

Ya amince cewa gyare-gyaren da ya fara aiwatarwa “sun kasance masu zafi a farko, amma a yau sakamakon yana bayyana.

“A hankali jama’a suna fahimta. Muna da ƙarin kuɗaɗe a cikin tattalin arziki, kuma babu cin hanci da rashawa.”

Don nuna gaskiya da adalci, ya yi nuni da Babban Bankin Nijeriya (CBN), inda ya ce: “Ba sai ka san wani ba kafin ka samu kuɗin waje da kake buƙata. ‘Yan wasa da karairayi sun fita daga kasuwa. A kasuwar kuɗin mu, ƙofa a buɗe take ga dukkan kasuwanni.”

“Idan muka duba, za mu ga cewa Jihar Kano, jiha ce da ta yi shura wajen batun kasuwaci da haɓɓakar tattalin arziki, don haka mu ƙara ƙaimi wajen ƙara tabbatar da wannan kambu ta fuskar da muke kai a yanzu,” inji Zango A Abdu.

Haka zalika ya kuma ba ta tabbacin Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano a shirye take wajen bada dukkan goyon bayan da ya kamata don samun nasarar wannan aiki.

By ukarofi