Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayyana shirinta na kafa rundunar yaƙi da ta’addanci mai ɗauke da sojoji 260,000 domin tunkarar barazanar tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin.
Shugaban ECOWAS, Omar Alieu Touray, wanda wakilinsa Abdel-Fatau Musah ya gabatar da jawabi a taron shugabannin rundunonin tsaro na Afirka da aka gudanar a Abuja, ya ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
“Babu wani yanki a Afirka da ya tsira daga ta’addanci, rikice-rikicen cikin gida da kuma koma-baya ta fannin ci-gaba,” inji Musah.
ECOWAS ta ce za ta buƙaci dala biliyan 2.5 a kowace shekara domin tallafa wa rundunar da kayan aiki da kuɗaɗen gudanarwa. Ana sa ran Ministocin kuɗi da na tsaro za su gana a ranar Juma’a domin kammala tsarin yadda za a samar da kuɗaɗen.
Touray ya ce yankin Sahel ya fi kowanne yanki fama da ta’addanci, inda ya ce kashi 51 cikin 100 na mutanen da suka mutu sakamakon ta’addanci a duniya a shekarar 2024 sun fito ne daga yankin.
A yayin da ECOWAS ke ci gaba da ƙoƙarin kafa rundunar sojoji 5,000 ƙarƙashin tsarin tsaro na Afirka, ana sa ran sabuwar rundunar za ta taimaka wajen ƙara ƙarfin yaƙi da ta’addanci.
Sai dai ba dukkan ƙasashen da aka gayyata suka halarci taron ba. Daga cikin ƙasashe 54 da aka gayyata, 36 ne suka samu wakilci.
Ko da yake Jamhuriyar Nijar ta halarta, Mali da Burkina Faso ba su halarta ba — lamarin da ba zai rasa nasaba da rikicin siyasa da ke tsakaninsu da ECOWAS ba.
Tsohon Firaministan Guinea, Lansana Kouyaté, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki na haɗin gwiwar tsaro a Afirka.
“Karon farko ne shugabannin rundunonin tsaro na dukkan ƙasashen Afirka suka haɗu. Wannan ya nuna muhimmancin batun — ba za a samu ci gaba ba sai da zaman lafiya,” inji shi.
Kouyaté ya buƙaci shugabannin Afirka da su haɗa kai wajen samar da tsaro, yana mai jaddada cewa Afirka ba ƙasa ɗaya ba ce, illa dai haɗin gwiwar ƙasashe masu bambancin tarihi da al’adu. Ya ce zai gabatar da shawarwari kan yadda za a samar da kuɗaɗen tsaro ta hanyar haɗin gwiwa da masu zaman kansu.
A nata ɓangaren, Mataimakiyar Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya, Amina Mohammed, ta buƙaci shugabannin Afirka da su ɗauki nauyin tsaron nahiyar.
Ta yi gargaɗin cewa ta’addanci, yaƙi ta kafar intanet da sauyin yanayi na barazana ga zaman lafiyar Afirka. Ta ƙara da cewa, “Afirka ta zama cibiyar mutuwar mutane sakamakon ta’addanci.
A cikin shekaru biyu kacal, hare-hare a ƙasashen gaɓar tekun yammacin Afirka sun ƙaru da kashi 250 cikin 100.”
Ta ce fiye da makarantu 14,000 sun rufe a yankin Sahel saboda rikici, sannan ta yi gargaɗi kan barazanar fasahar zamani da sauyin yanayi, ciki har da faduwar ruwan tafkin Chadi da ta raba fiye da mutane miliyan uku da muhallinsu.
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya buƙaci a samar da sabuwar dokar tsaro ta nahiyar Afirka da za ta dogara da amincewa, musayar bayanan sirri da haɗin gwiwa.
“Wannan taro bai kamata ya ƙare da tafi ba kawai a watse. Ya zama ginshiƙin sabuwar tsarin tsaro na Afirka,” inji shi.
Ya buƙaci a kafa taron dindindin na shugabannin rundunonin tsaro na Afirka da kuma zuba jari a fannin ƙirƙire-ƙirƙire na tsaro da fasahar zamani.
A ƙarshe, tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana cewa akwai fiye da ƙungiyoyin ’yan tada ƙayar baya 1,000 a nahiyar Afirka, yana mai kira da a ƙara ƙarfafa masana’antar tsaro da ƙirƙirar fasahohin gida.
