
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Ribas ta fara gudanar da shirye-shiryen koma wa mulkin dimukraɗiyya daga na dokar ta-ɓaci a jihar.
Sakataren gwamnatin, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya sanar da haka a wata takarda.
A cewarsa, an gayyaci baki ɗaya masu ruwa da tsaki zuwa interdenominatuonal church thanksgiving service a yau Lahadi.
Waɗanda aka gayyata sune manyan sakatarori, ciyamomin ƙananan hukumomi, jagororin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, jagororin hukumomi da sauransu.
Kantoman jihar, Ibok-Ete Ibas shi ne baƙo na musamman a taron.
